DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, September 15, 2026
HomeLabaraiTallafin fetur ba zai dawo ba - Gwamnatin Nijeriya

Tallafin fetur ba zai dawo ba – Gwamnatin Nijeriya

Gwamnatin Nijeriya ta bayyana cewa kiran da tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar ya yi na dawo da tallafin man fetur zai durƙusar da garambawul da sauye-sauyen da aka riga aka cimma a fannin man fetur na ƙasar.

Kamfanin dillancin labarai na ƙasa (NAN) ya ruwaito cewa gwamnatin ta bayyana hakan ne a matsayin martani ga shirin da Atiku ya bayyana na dawo da tallafin fetur idan har aka zaɓe shi a matsayin shugaban ƙasa a babban zaɓen 2027.

Gwamnatin ta ƙara da cewa matakin zai haifar da sarƙaƙiyar shari’a da ta kasafin kuɗi, tare da tsoratar da masu zuba jari a matatun mai na cikin gida da suka haɗa da matatar Dangote da sauran ƙananan matatu.

Babban mai ba shugaban ƙasa shawara kan yaɗa labarai, Bayo Onanuga, ya bayyana shirin na Atiku a matsayin koma-baya da kuma alamun “matsananciyar sha’awar son lashe zaɓen shugabancin ƙasa”, yana mai cewa yanayin kasuwar man fetur ta Nijeriya ya sauya sosai tun bayan da Shugaba Bola Tinubu ya sanar da janye tallafin a ranar 29 ga watan Mayun 2023.

A nasa ɓangaren, Ministan Kuɗi Taiwo Oyedele, ya bayyana cewa cire tallafin fetur ya samar wa asusun Nijeriya kusan naira tiriliyan 15.8 tsakanin watan Yunin 2023 zuwa Disambar 2025, inda gwamnatin tarayya ta sami naira tiriliyan 5.4, yayin da aka raba naira tiriliyan 10.4 a tsakanin gwamnatocin jihohi da na ƙananan hukumomi.

Shi ma Shugaba Bola Tinubu, yayin da yake karɓar baƙuncin Gwamna Ademola Adeleke na jihar Osun a fadar shugaban ƙasa, ya bayyana cewa shirin Atiku na mayar da tallafin fetur shaida ce ta ƙarancin fahimtarsa kan harkokin mulki da tattalin arziki.

Atiku Abubakar, wanda shi ne ɗan takarar shugaban ƙasa na babbar jam’iyyar adawa ta ADC, ya bayar da hujjar cewa ‘yan Nijeriya ba su ga amfanin cire tallafin ba, inda kuɗaɗen da aka tara ba su sauya halin talauci ko samar da abinci a kwanon talakawa ba bayan tashin farashin fetur daga ƙasa da naira 200 zuwa sama da naira 1,000.

Ya ce tsarinsa ba wai zai dawo da tsohon tsarin tallafi marar kyakkyawan tsari ba ne, a’a, wani tsari ne na musamman da zai tallafa wa matatun cikin gida tare da tabbatar da cewa an sauƙaƙa farashin ɗanyen mai domin amfanin masu saye.

Sai dai masana tattalin arziki da suka haɗa da shugaban cibiyar malaman kasuwar hannun jari ta ƙasa (CMAN), Farfesa Uche Uwaleke, da Farfesa Ken Ife, sun soki batun komawa tsohon tsarin tallafi, suna masu cewa ba a tallafa wa abubuwan da ake amfani da su, face dai fannin da ke samar da kayayyaki.

Sun gargaɗi cewa ciyo bashi domin biyan tallafi ya saɓa wa Dokar Kula da Kashe Kuɗaɗen Gwamnati (Fiscal Responsibility Act) kuma hakan na iya sake buɗe ƙofofin ɓarnatar da dukiyar ƙasa.

A gefe guda kuma, wasu ma’aikatan gwamnati irin su Ibrahim Abbas da tsohon ma’aikaci mai ritaya, Sule Aliu, sun nuna cewa talakawa da ma’aikata na ci gaba da fuskantar tsananin matsin tattalin arziki da karyewar darajar naira tun bayan cire tallafin, lamarin da ya sa shawarar da Atiku ya gabatar ta zama abin sha’awa ga talakawan ƙasar.

Ukashatu Wakili
Ukashatu Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili is a journalist and media professional serving as Deputy Managing Editor and Internship Coordinator at DCL Hausa. He has extensive experience in broadcast and digital journalism, with expertise in news reporting, editorial production, newsroom coordination and journalist training. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Usmanu Danfodiyo University, Sokoto.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata