DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, September 15, 2026
HomeSiyasaJigon LP ya kai WAEC, UNN da NYSC kotu kan takardun karatun...

Jigon LP ya kai WAEC, UNN da NYSC kotu kan takardun karatun Peter Obi

Wani babban jigo a jam’iyyar Labour Party (LP), Abayomi Arabambi, ya shigar da ƙarar hukumar jarrabawa ta yammacin Afirka (WAEC), Jami’ar Nijeriya da ke Nsukka (UNN), da kuma hukumar kula da masu ui wa ƙƘasa hidima (NYSC) a gaban kuliya kan takardun shaidar karatun ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa Arabambi, ta cikin ƙorafi guda uku daban-daban da lauyansa Anderson Asemota ya shigar a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, yana neman umarnin kotu da zai tilasta wa waɗannan hukumomi uku fitar da bayanan sirri na hukuma da ke da alaƙa da takardun shaidar karatun da ake iƙirarin an bai wa Obi.

Mai ƙarar ya shigar da ƙararrakin ne a ƙarƙashin dokar ‘yancin samun bayanai ta 2011, inda ya yi zargin cewa hukumomin sun ƙi ko sun kasa amsa buƙatunsa na neman bayani kan tarihin karatun Obi domin tabbatar da gaskiya da kuma nuna kyakkyawan shugabanci ga masu neman ofisoshin gwamnati.

Ƙarar da aka shigar a kan WAEC mai lamba FHC/ABJ/CS/2064/2026 da ta NYSC mai lamba FHC/ABJ/CS/2063/2026 an shigar da su ne a ranar 1 ga watan Satumban 2026, yayin da ƙarar da aka shigar a kan jami’ar UNN mai lamba FHC/ABJ/CS/2144/2026 aka shigar da ita a ranar 9 ga watan Satumban 2026.

Arabambi ya jaddada cewa ba wai yana neman kotu ta yanke hukunci a kan ko takardun da Obi ya miƙa wa hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) domin zaɓen shugaban ƙasa na 2027 na bogi ne ko na gaskiya ba, a’a, yana neman hukumomin ne su bayyana ainihin bayanan da ke cikin kundinsu domin tantance sahihancin takardun.

A ƙarar da ya shigar a kan WAEC, yana neman kotu ta tilasta wa hukumar sakin kwafin sahihiyar takardar shaidar WAEC mai lamba SC042560 da aka ba Obi Gregory Onwubuase a watan Yunin 1978. Ga UNN kuma, yana neman bayanan rijistar digiri da hukumar majalisar jami’ar ke da su kan takarda mai lamba D000198. Haka kuma a ɓangaren NYSC, yana neman bayanan takardar shaidar hidimar ƙasa mai lamba 203495 da aka ba “Obi, Gregory Peter-Onwubuase” a ranar 1 ga watan Mayun 1986 da kuma yadda sunan ya fito a cikinta.

Takardun kotun sun nuna cewa WAEC ta ƙi amincewa da buƙatarsa a wata wasiƙa mai kwanan wata 11 ga watan Agustan 2026 tana mai kafa hujja da wasu sassa na dokar ‘yancin samun bayanai, yayin da UNN da NYSC ba su ma ba shi amsa ba ballantana bayyana dalilinsu na ƙin amincewa.

Ukashatu Wakili
Ukashatu Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili is a journalist and media professional serving as Deputy Managing Editor and Internship Coordinator at DCL Hausa. He has extensive experience in broadcast and digital journalism, with expertise in news reporting, editorial production, newsroom coordination and journalist training. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Usmanu Danfodiyo University, Sokoto.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata