Rundunar sojin Nijeriya ta tabbatar da sace wasu malaman addinin Musulunci a jihar Zamfara, yayin da ta ƙaryata jita-jitar da ke yawo cewa an sace su ne a gidan tsohon gwamnan jihar, Sanata Abdul’aziz Yari, da ke ƙaramar hukumar Talata Mafara.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa rundunar sojin ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da muƙaddashin mataimakin daraktan hulɗa da jama’a na rundunar soji ta Sashe na 8/Yanki na 2 na rundunar Operation FANSAN YAMMA, Laftanar Kanal Olaniyi Osoba, ya fitar a ranar Lahadi.
Sanarwar, mai taken “Rahoton halin da ake ciki kan sace malaman addinin Musulunci a jihar Zamfara,” ta bayyana cewa an sace mutanen ne a kan hanyarsu ta zuwa Talata Mafara daga yankin dajin Sububu da ke cikin ƙaramar hukumar Bakura, ba wai a gidan Sanata Yari ba.
Kamar yadda rahoton jaridar Daily Trust da aka ambata a labarin ya bayyana, ’yan bindiga sun sace limaman masallatan Juma’a shida ne a kan hanyarsu ta zuwa Talata Mafara domin halartar wani zaman addu’a na musamman da aka shirya domin zaman lafiya da kuma samun nasarar neman tazarce na Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027.
Rahoton ya ƙara da cewa an sace malaman ne a nisan kusan kilomita uku daga ƙauyen Damri, a yankin Gidan Suleiman Bature da ke cikin dajin Gonar Sarki.
Kakakin rundunar ’yan sandan jihar Zamfara, DSP Yazid Abubakar, shi ma ya tabbatar da adadin limaman da aka sace su shida ne, inda ya bayyana cewa jami’an tsaro sun ƙarfafa ayyukan ceto domin ganin sun kuɓutar da su cikin ƙoshin lafiya.
Rundunar sojin ta bayyana cewa dakarunta na ci gaba da aiki kafaɗa-da-kafaɗa da sauran hukumomin tsaro da hanyoyin tattara bayanan sirri domin ceto malaman, tare da yin kira ga al’umma da su yi watsi da labaran ƙanzon ƙurege da ba a tantance ba, su kuma ci gaba da bai wa jami’an tsaro ingantattun bayanai.
