DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, September 15, 2026
HomeBabban Labari Muna da dalilan kin fitar da bayanan sirri kan binciken Tinubu -...

Muna da dalilan kin fitar da bayanan sirri kan binciken Tinubu – FBI

Hukumar binciken manyan laifuka ta Amurka (FBI) ta nemi wata kotun Amurka ta ba ta izinin gabatar da bayanan sirri domin bayyana dalilin da ya sa ta hana fitar da wasu bayanan bincike da suka shafi zargin safarar miyagun kwayoyi da ake dangantawa da shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu.

A cikin wata takarda da FBI ta shigar a ranar 20 ga Agusta a gaban kotun gundumar Amurka ta ‘District of Columbia’, hukumar ta ce ba za ta iya bayyana a bainar jama’a dukkan dalilan da suka sa ta hana fitar da bayanan ba.

Saboda haka, hukumar ta nemi kotun ta ba ta damar gabatar da rubutaccen bayani da za a mika wa alkalin kotu a asirce, ba tare da sanya shi cikin bayanan kotun da jama’a za su iya gani ba.

FBI ta ce sakin bayanan da ta boye na iya tona asirin dabaru da hanyoyin da jami’an tsaro ke amfani da su wajen gudanar da bincike, tare da yiwuwar jefa rayuka ko lafiyar wasu mutane cikin hadari, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Kamfanin neman goyon bayan siyasa na Washington, ‘Von Batten-Montague-York’, wanda kwanan nan ya samu aiki daga dan takarar shugaban Nijeria na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ne ya wallafa takardar a shafinsa na X.

A cewar FBI, bayanan da ake magana a kansu na da alaka da bukatun neman bayanai guda biyu karkashin dokar neman bayanai ta ‘Freedom of Information Act’ (FOIA).

Bukatar farko, mai lamba 1588244-000, ta nemi “cikakken kundin FBI” da ya shafi Tinubu, wanda aka bayyana a cikin bukatar a matsayin zababben shugaban Nijeriya a watan Fabrairun 2023.

Bukatar ta biyu, mai lamba 1593615-000, ta nemi bayanan tambayoyin bincike na FBI Form 302 da suka shafi Tinubu, daga shari’ar FBI mai lamba 245-IP-71386-UUUUUU, a shekarun 1992 da 1993.

FBI ta ce ta dogara da wasu keɓancewa da dokar FOIA ta tanada, ciki har da sashe na 6, 7(C), 7(D), 7(E) da 7(F), wajen hana fitar da wasu sassan bayanan.

Hukumar ta ce sakin bayanan na iya, a tsakanin sauran abubuwa, bayyana dabaru da hanyoyin gudanar da bincike ko kuma yin barazana ga rayuwa ko lafiyar wani mutum.

FBI ta kuma shaida wa kotun cewa ba za ta iya bayyana cikakken dalilin amfani da sashe na 7(E) da 7(F) a cikin bayanan da jama’a za su gani ba.

Don haka, ta nemi izinin kotun domin gabatar da wani karin bayani na sirri, wanda za a rufe daga jama’a, domin bayyana matsayinta ga alkalin.

FBI ta ce idan kotun ta amince da bukatarta, za ta gabatar da bayanan sirrin kafin 28 ga Agusta, 2026.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata