Hukumar lafiya ta duniya (WHO) ta ce akwai karancin haɗarin ɓarkewar cutar Ebola a Nijeriya idan aka kwatanta da wasu ƙasashen makwabta a yammacin Afirka, tana mai cewa hukumomin lafiya sun ƙara ƙaimi wajen dakile yaduwar cutar a yankunan da abin ya shafa.
Babban daraktan mai kula da shirin gaggawa na WHO, Chikwe Ihekweazu, ne ya bayyana hakan a ranar Talata yayin wata hira da ya yi a shirin Morning Show na Arise Television.
A cewarsa, ƙasar Uganda ce kaɗai a wajen DR Congo da aka tabbatar da samun masu ɗauke da cutar Ebola.
Duk da cewa haɗarin barkewar cutar a Nijeriya bai yi yawa ba, Ihekweazu ya jaddada cewa annobar na ci gaba da zama babbar barazana ga lafiyar duniya, wadda ke buƙatar haɗin gwiwar ƙasashe wajen magance ta.
Jami’in na WHO ya ƙara da cewa wannan ne karo na uku kacal da annobar Ebola ta kai matsayin da ya sa aka ayyana ta a matsayin irin wannan matakin gaggawar lafiya ta duniya.
