Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya bukaci ‘yan Nijeriya da kada su yanke ƙauna kan matsalolin tsaro, yana mai cewa wajibi ne a ci gaba da addu’a domin a gano tare da fallasa masu ɗaukar nauyin ta’addanci da sauran miyagun laifuka a ƙasar.
Kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito, Akpabio ya bayyana hakan ne a wajen taron addu’ar mabiya addinin Kirista da aka gudanar a Cibiyar Kiristoci ta Ƙasa da ke Abuja domin bikin cika shekaru 27 na mulkin dimokuraɗiyya a Nijeriya.
Akpabio ya ce lokacin da yake gwamnan jihar Akwa Ibom kimanin shekaru 19 da suka gabata, ya ƙaddamar da addu’ar wata-wata domin tunkarar matsalolin garkuwa da mutane, tada ƙayar baya da kashe-kashe da suka addabi jihar a lokacin.
Ya ce dole ne a ci gaba da addu’a domin Allah ya tona asirin masu aikata miyagun laifuka da kuma masu ɗaukar nauyinsu, ko suna cikin gwamnati ko a wajen gwamnati. A cewarsa, ya kamata masu tallafa wa ta’addanci su rasa kwanciyar hankali har sai an yi galaba a kansu.
Akpabio ya amince cewa rashin tsaro na ci gaba da jefa al’ummomi cikin fargaba, inda manoma ke tsoron komawa gonakinsu, matafiya ke tafiya cikin rashin tabbas, yayin da iyalai da dama ke jimamin rasa ‘yan uwansu sakamakon hare-hare da ayyukan ta’addanci.
Ya ce duk da ƙalubalen da ƙasar ke fuskanta, Nijeriya ta tsallake matsaloli da dama a baya, ciki har da rikice-rikicen siyasa, annobar Ebola da COVID-19, da kuma hare-haren masu tayar da ƙayar baya, yana mai bayyana cewa ƙasar za ta shawo kan matsalolin da ake ciki a yanzu.
Shugaban Majalisar Dattawan ya kuma nuna alhininsa kan halin da yara da aka sace ke ciki, yana mai cewa wahalar da iyayensu ke sha na da matuƙar raɗaɗi. Ya tabbatar da cewa gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na ci gaba da ƙoƙarin dawo da zaman lafiya da kuma ceto duk mutanen da ke hannun masu garkuwa da mutane.
