DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Wednesday, July 8, 2026
HomeLabaraiNUT reshen Oyo ta shiga yajin aiki kan sace dalibai da malamai...

NUT reshen Oyo ta shiga yajin aiki kan sace dalibai da malamai a jihar

Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya bayar da umarnin girke jami’an tsaron gandun daji 1,000 a jihar Oyo.

Haka kuma, ya umarci wata rundunar tsaro ta musamman da ta ƙara ƙaimi wajen kubutar da ɗalibai da malaman da aka sace daga makarantu uku da ke karamar hukumar Oriire.

Wannan na zuwa ne yayin da kungiyar Malamai ta Nijeriya NUT ta ayyana yajin aikin sai baba-ta-gani a jihar, tare da sanar da shirinta na gudanar da gangamin nuna goyon baya a faɗin ƙasar domin matsa wa gwamnati lamba ta kubutar da mutanen da aka yi garkuwa da su.

Yajin aikin ya fara daga Litinin, 1 ga Yunin 2026, saboda gazawar da suka ce an yi wajen ganin an sako waɗanda aka sace, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

A cikin wata takarda da shugaban ƙungiyar na ƙasa Audu Amba, da babban sakatarenta, Clinton J. Ikpitibo, suka sanya wa hannu, ƙungiyar ta bayyana matuƙar damuwarta kan abin da ta kira mummunan yanayi mai firgitarwa da kuma raɗaɗin da waɗanda aka sace ke fuskanta a yayin da suke tsare a hannun masu garkuwa da mutane.

Sai dai wata sanarwa da mai ba shugaba Tinubu shawara na musamman kan yaɗa labarai Bayo Onanuga ya sanya wa hannu ranar Lahadi, ta bayyana cewa wata babbar tawagar gwamnatin tarayya ta isar da umarnin shugaban ƙasar ga shugabannin al’umma da ’yan majalisa yayin wata ziyara da suka kai wa al’ummomin Esiele da Yawota da ke karamar hukumar Oriire a ranar 31 ga Mayun 2026.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata