Mai bai wa Shugaba Tinubu shawara kan harkokin yaɗa labarai Bayo Onanuga, ya soki ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC Atiku Abubakar, bisa rashin yin martani bayan kubutar da ɗalibai da malamai da aka sace a ƙaramar hukumar Oriire ta Jihar Oyo.
A cewarsa Atiku bai fito ya taya gwamnatin tarayya, jami’an tsaro da kuma iyalan waɗanda aka kuɓutar murna ba.
A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X ranar Asabar, Onanuga ya ce Atiku ya shafe tsawon lokaci yana sukar gwamnatin Shugaba Tinubu yayin da ɗaliban da malamansu ke hannun masu garkuwa da mutane, amma ya yi shiru bayan da aka samu nasarar kuɓutar da su.
Ya kuma yi zargin cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya riƙa amfani da batun satar ɗaliban a matsayin makamin yaƙin neman zaɓe.
Sai dai Onanuga ya yabawa ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC Peter Obi, kan damuwan da ya nuna bayan ceto ɗaliban.
A cewar jaridar Punch, ya ce ko da yake Obi bai yaba wa Shugaba Tinubu kai tsaye ba, amma ya yi kira da a gode wa Allah tare da yaba wa jami’an tsaron da suka taka muhimmiyar rawa wajen kuɓutar da waɗanda aka sace.
An sace ɗalibai 39 da malamai bakwai ne a ranar 15 ga Mayu 2026, bayan da ‘yan bindiga suka kai hare-hare a Community Grammar School da Baptist Nursery and Primary School da ke ƙaramar hukumar Oriire a Jihar Oyo.
A lokacin da suke tsare, ɗaya daga cikin malamansu, Michael Oyedokun, ya rasa ransa a hannun masu garkuwa da su.
Kafin a kuɓutar da su, Atiku ya sha yin kira ga gwamnati ta gaggauta ceton ɗaliban, tare da sukar yadda ake tafiyar da lamarin.
Haka kuma ya bayyana rabon shinkafa ga iyalan waɗanda abin ya shafa a matsayin matakin da ba zai maye gurbin ceton mutanen ba, yana mai zargin gwamnati da rashin nuna isasshen ƙwazo wajen magance matsalar.
Da yake sanar da nasarar aikin ceton a ranar Juma’a, Onanuga ya ce ba a yi wata tattaunawa da masu garkuwa da mutanen ko biyan kuɗin fansa ba.
Ya ƙara da cewa an kama mutane takwas da ake zargi suna da hannu a lamarin tare da miƙa su ga Hukumar tsaro ta DSS, yayin da aka hallaka wasu daga cikin ‘yan ƙungiyar.
