DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Wednesday, September 23, 2026
HomeLabaraiAnnobar zazzabin Aladu ta yi wa manoma mummunar ɓarna a Filato

Annobar zazzabin Aladu ta yi wa manoma mummunar ɓarna a Filato

Manoman da ke kiwon aladu a Jihar Filato sun nuna matuƙar damuwa kan barkewar cutar African Swine Fever wacce ta hallaka dubban aladu tare da tilasta rufe daruruwan wuraren kiwonsu.

Sun ce annobar ta jawo asarar dukiya ta biliyoyin naira, lamarin da ke barazana ga dorewar masana’antar kiwon aladu a jihar.

A cikin wata budaddiyar wasika da suka aike wa Gwamna Caleb Mutfwang, masu ruwa da tsaki a harkar sun buƙaci gwamnatin jihar Plateau ta gaggauta ɗaukar matakan ceto masana’antar kafin ta durƙushe gaba ɗaya.

Sun bayyana cewa kiwon aladu na taka muhimmiyar rawa wajen samar da abinci, ayyukan yi da kuma ƙarfafa tattalin arzikin Filato.

Babban jami’in kamfanin Topnotch Pig Farms and Services kuma ƙwararren likitan dabbobi a Saction Hub Limited,Joseph Yonkpa ya ce, annobar ta riga ta kashe dubban aladu duk da cewa har yanzu ba a tantance adadin daidai ba.

Ya ƙara da cewa manya da ƙananan gonakin kiwo sun fuskanci matsalar, inda da dama daga cikin manyan gonakin jihar suka dakatar da ayyukansu.

Yonkpa ya bayyana lamarin a matsayin babbar masifa, yana mai cewa Filato na daga cikin manyan jihohin da ke samar da naman alade a Najeriya, tare da kai kayayyaki zuwa jihohin Kaduna da Nasarawa da kuma wasu sassan kudancin ƙasar.

Ya ce dubban manoma, ma’aikata, masu safara, masu sarrafa nama da ‘yan kasuwa na dogaro da wannan sana’a wajen samun abin rayuwa.

Ya kuma bayyana cewa cutar African Swine Fever na da saurin yaɗuwa sosai, kuma har yanzu ba ta da magani ko allurar rigakafi.

A cewarsa annobar, ta haddasa faɗuwar farashin naman alade zuwa ƙasa da naira 2,000 kan kowane kilo saboda firgici da kuma raguwar kwarin gwiwar masu saye.

Hakan, a cewarsa, ya sa masu kiwo suka kasa sake farfaɗo da gonakinsu a wannan mawuyacin yanayin tattalin arziki.

Domin shawo kan matsalar, Yonkpa ya buƙaci Gwamna Mutfwang ya kafa kwamitin gaggawa ta hannun ma’aikatar raya kiwon dabbobi, ayyukan likitocin dabbobi da kifi.

Ya ce kwamitin zai tantance girman barnar da aka yi, ya samar da kayan kariya, tallafin fasaha da agaji ga manoman da abin ya shafa, tare da tsara shirin farfaɗo da masana’antar.

Ya yi gargadin cewa idan ba a ɗauki matakin gaggawa ba, annobar za ta iya jefa wani muhimmin ɓangare na tattalin arzikin Filato cikin matsanancin koma baya, tare da ƙara ta’azzara matsalar ƙarancin abinci da rashin aikin yi. Duk da haka, ya ce manoman na da kyakkyawan fata cewa gwamnatin jihar za ta gaggauta ɗaukar matakan da suka dace domin ceto masana’antar kiwon Aladu daga rugujewa baki ɗaya.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata