Ɗan takarar shugabancin Nijeriya na jam’iyyar NDC, Peter Obi, da tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, sun taya Gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke, murnar sake lashe zaɓen gwamnan jihar.
Jaridar PUNCH ta ruwaito cewa hukumar zaɓen Nijeriya INEC ta ayyana Adeleke a matsayin wanda ya lashe zaɓen da aka gudanar ranar Asabar, bayan ya samu ƙuri’u 511,067.
Adeleke, wanda ya tsaya takara a ƙarƙashin jam’iyyar Accord, ya doke ɗan takarar APC, Bola Oyebamiji, wanda ya samu ƙuri’u 444,815.
A cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, Peter Obi ya taya Adeleke da al’ummar Osun murnar nasarar, yana mai cewa sakamakon zaɓen ya nuna cewa ikon zaɓar shugabanni yana hannun jama’a.
Obi ya kuma yaba wa matasan Osun kan yadda ya ce suka tsaya tsayin daka wajen kare haƙƙinsu na zaɓe cikin lumana.
Ya ce sakamakon zaɓen Osun ya kamata ya zama darasi gabanin zaɓen 2027, inda ya buƙaci ’yan Nijeriya su kasance masu taka rawa wajen kare ƙuri’unsu.
Obi ya kuma yi kira ga ’yan siyasa da su fifita muradun jama’a, tare da gudanar da siyasa cikin zaman lafiya da bin doka.
A nasa ɓangaren, Bukola Saraki ya bayyana sake zaɓen Adeleke a matsayin ƙuri’ar amincewa da al’ummar Osun suka sake ba shi bayan sun shafe shekaru huɗu suna kallon yadda yake tafiyar da mulkin jihar.
Saraki ya ce al’ummar jihar sun samu damar tantance ayyukan gwamnan, da kuma kwatanta alkawuran da ya ɗauka da abubuwan da ya aiwatar, kafin su yanke shawarar ba shi damar ci gaba da mulki.
Tsohon shugaban majalisar dattawan ya kuma yaba wa al’ummar Osun kan kaɗa ƙuri’a tare da kasancewa cikin shiri wajen kare ƙuri’unsu.
Saraki ya buƙaci Adeleke ya yi amfani da wa’adin mulkinsa na biyu wajen ƙara inganta ayyukan da ya fara, da kuma tabbatar da cewa ya cancanci amincewar da al’ummar jihar suka sake ba shi.
