DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Wednesday, April 22, 2026
HomeSiyasaPRP a Bauchi na zawarcin Gwamnan jihar

PRP a Bauchi na zawarcin Gwamnan jihar

Jam’iyyar PRP a jihar Bauchi ta yi kira ga Gwamnan jihar, Bala Abdulkadir Mohammed, da ya koma jam’iyyar domin ciyar da jihar da dimokuraɗiyyar Nijeriya gaba.

A wani taron manema labarai da shugaban jam’iyyar na jihar, Abdurrahman Yusuf Mu’azu, ya jagoranta a Bauchi, ya ce jam’iyyar a shirye take ta karɓi gwamnan tare da magoya bayansa, tana mai tabbatar musu da aminci da babu rikici ko na shari’a a cikinta.

Ya ce jam’iyyar na da burin bai wa gogaggun ‘yan siyasa dama su ci gaba da bayar da gudunmawa, yana mai cewa ko da hakan zai sa su sadaukar da wasu mukamai domin tabbatar da haɗin kai.

Wannan kira na zuwa ne yayin da ake rade-radin cewa gwamnan na iya ficewa daga jam’iyyar PDP, inda wasu jam’iyyu kamar NNPP da ADC suma ke ƙoƙarin jan hankalinsa.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata