DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Wednesday, July 8, 2026
HomeLabaraiKotu ta yi barazanar ɗaure shugaban INEC da Samuel Anyanwu

Kotu ta yi barazanar ɗaure shugaban INEC da Samuel Anyanwu

Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta gargadi shugaban hukumar zaɓen Nijeriya INEC, Farfesa Joash Amupitan, da sakataren jam’iyyar PDP, Sanata Samuel Anyanwu, kan yiwuwar dauresu idan suka gaza bin umarnin kotu.

Jaridar Punch ta rawaito cewa kotun ta fitar da sanarwa, inda ta jaddada hukuncin da ta yanke tun ranar 12 ga Janairu, wanda ya kori Anyanwu daga jam’iyyar PDP, kamar yadda aka tabbatar.

Kotun ta bayyana cewa idan Anyanwu da shugabannin INEC suka ci gaba da kin bin wannan hukunci, za a iya tuhumar su da raina kotu, wanda zai iya kai su ga dauri zuwa kurkuku.

Hakan na zuwa ne yayin da ake fama da rikicin shugabanci a PDP, wanda ya raba jam’iyyar gida biyu masu takaddama kan halaccin shugabanci.

A gefe guda, bangaren jam’iyyar da Kabiru Tanimu Turaki ke jagoranta ya bukaci INEC da ta daina amincewa da Anyanwu a matsayin sakataren PDP, yana mai cewa tun bayan korarsa, ba shi da hurumin wakiltar jam’iyyar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata