Farashin ɗanyen mai a kasuwannin duniya ya ragu zuwa kusan dala 70 kan ganga, lamarin da ya sake haifar da tsammanin cewa farashin fetur a Nijeriya zai iya sauka nan ba da jimawa ba.
A safiyar Alhamis, farashin danyen mai ya ragu daga dala 71 zuwa dala 70 kan ganga, bayan ci gaba da faduwar farashin a kasuwannin duniya.
Sai dai duk da wannan raguwar, farashin litar fetur a Nijeriya bai sauya ba, abin da ya jawo ƙorafe-ƙorafe daga masu amfani da man fetur.
Masana sun danganta raguwar farashin ɗanyen mai da ƙarancin buƙata a kasuwannin duniya, sassaucin rikice-rikicen siyasa a wasu yankunan da ake hako mai da kuma hasashen ƙarin samar da mai daga manyan ƙasashe masu fitar da shi.
Tun bayan sassauta kasuwar man fetur a Nijeriya, ana sa ran sauyin farashin ɗanyen mai a duniya zai riƙa tasiri kan farashin man fetur a cikin gida.
Hakan ya sa mutane da dama ke tambayar dalilin da ya sa har yanzu ba a rage farashin fetur ba duk da ci gaba da faduwar farashin ɗanyen mai.
Ma’aikatar Albarkatun Man Fetur da Hukumar Kare Haƙƙin Masu Amfani da Kaya da Hana Cin Zarafi (FCCPC) sun bukaci ‘yan kasuwar mai su rage farashin fetur domin jama’a su amfana da raguwar farashin ɗanyen mai.
Shugaban FCCPC, Tunji Bello, ya bayyana cewa hukumar ba ita ce ke ƙayyade farashin fetur ba, amma tana da alhakin kare masu amfani da kaya daga duk wani cin zarafi ko rashin adalci a kasuwa.
Ya ce abin da ke damun hukumar shi ne yadda masu kasuwancin mai ke saurin ƙara farashi idan ɗanyen mai ya yi tsada, amma suke jinkirin rage shi idan farashin ya sauka.
A halin yanzu, duk da raguwar farashin ɗanyen mai zuwa dala 70 kan ganga, ana ci gaba da sayar da litar fetur sama da naira 1,200 a Legas, yayin da a wasu sassan Nijeriya farashin ke kusan naira 1,300 kan lita.
