DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Wednesday, July 8, 2026
HomeLabarai'Ranar Dimokuraɗiyya ta bana za mu nuna nasarorin gwamnatin Tinubu'

‘Ranar Dimokuraɗiyya ta bana za mu nuna nasarorin gwamnatin Tinubu’

Gwamnatin Nijeriya ta ce bikin Ranar Dimokuraɗiyya ta bana zai zama wata dama ta nuna nasarorin da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta samu da kuma ci gaban da aka samu wajen ƙarfafa dimokuraɗiyya da bunƙasa ƙasa.

Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume, ne ya bayyana hakan ranar Talata a Abuja yayin ƙaddamar da Kwamitin Tsare-tsare na Ma’aikatu (IMC) domin shirya bikin Ranar Dimokuraɗiyya karo na 27.

Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, Akume ya ce bikin ranar 12 ga Yuni zai bai wa gwamnati damar bayyana wa ‘yan Nijeriya irin ci gaban da aka samu wajen ƙarfafa dimokuraɗiyya, aiwatar da sauye-sauye da kuma sake fasalin ƙasa duk da ƙalubalen tattalin arziki da ake fuskanta.

Akume ya bayyana ranar Dimokuraɗiyya a matsayin lokaci na tunawa da tafiyar dimokuraɗiyyar Nijeriya da kuma sabunta alƙawarin gwamnati na kare ƙa’idojin dimokuraɗiyya da tabbatar da ci gaba mai ɗorewa.

Ya kuma karrama jaruman gwagwarmayar ranar 12 ga Yunin 1993 musamman marigayi Cif Moshood Kashimawo Olawale (MKO) Abiola, yana mai cewa sadaukarwarsu ce ta taimaka wajen tabbatar da ranar 12 ga Yuni a matsayin Ranar Dimokuraɗiyyar Nijeriya.

Ukashatu Wakili
Ukashatu Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata