DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Monday, October 5, 2026
HomeLabaraiSamun kujerar gaba a majalisar ɗinkin duniya ba ƙaramin abu ba ne...

Samun kujerar gaba a majalisar ɗinkin duniya ba ƙaramin abu ba ne ga Nijeriya – Jimoh Ibrahim

Jakadan Nijeriya na dindindin a majalisar ɗinkin duniya, Jimoh Ibrahim, ya ce samun damar Nijeriya ta zauna a sahun gaba a babban taron majalisar ɗinkin duniya karo na 81 ba ƙaramin abu ba ne, yana mai cewa ya cika alkawarin da ya yi na tabbatar da muhimmiyar kujerar ƙasar.

Da yake magana a shirin Politics Today na gidan Talabijin na Channels, Ibrahim ya ce bai goyi bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya je birnin New York ba bayan da aka tabbatar cewa sama da kashi 60 cikin 100 na waɗanda aka tsara za su yi jawabi sun samu wakilcin mataimakansu ko Ministocin harkokin wajen ƙasashensu.

Ibrahim ya ce ganin cewa shugabannin ƙasashe da dama ba su halarci taron da kansu ba, bai ga dalilin da ya sa Shugaba Tinubu ya bar wasu muhimman al’amuran cikin gida domin zuwa New York ya yi jawabi na kusan mintuna 15 ba.

Ya kuma yi nuni da cewa shugabannin Afirka ta Kudu, China da Rasha, da wasu ƙasashe, ba su halarci taron da kansu ba, yayin da mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya jagoranci tawagar Nijeriya tare da wakiltar Tinubu a taron.

Jakadan ya dage cewa Shettima ya wakilci Nijeriya yadda ya kamata, inda ya gabatar da jawabin ƙasar a babban taron majalisar ɗinkin duniya tare da halartar wasu muhimman taruka da ganawa.

Ibrahim ya kuma kare ikirarinsa na baya cewa ya samu damar tabbatar da Nijeriya ta zauna a wani muhimmin wuri a sahun gaba a babban zauren majalisar ɗinkin duniya.

Ya ƙara da cewa ikirarinsa na Nijeriya ta zauna kusa da Shugaban Amurka Donald Trump bai kasance kamar yadda wasu suka fahimta ba, domin Trump ya shiga zauren ne don gabatar da jawabi sannan ya fita ba tare da zama a kujerar da aka tanada ba.

A cewar Ibrahim, da Trump ya zauna a zauren bayan jawabin nasa, da ba lallai ne ya kasance kusa da Nijeriya ba, yana mai cewa Nijeriya ta samu matsayi na shida a sahun gaba.

Ya ce samun irin wannan matsayi a zauren majalisar ɗinkin duniya ba abu ne mai sauƙi ba, musamman ganin yadda tsarin zama ke bai wa ƙasashe matsayi daban-daban a babban taron.

Sanatan ya kuma ce Shugaba Tinubu zai samu damar gabatar da jawabi a majalisar ɗinkin duniya a lokacin da ya dace, duk da cewa bai halarci taron karo na 81 ba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata