Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya bar birnin Paris na ƙasar Faransa, inda ya kammala hutun aiki da ya kwashe kwanaki yana yi, kuma yanzu yana kan hanyarsa ta komawa Nijeriya.
Fadar shugaban ƙasar ta bayyana cewa jirgin shugaban ƙasar ana sa ran zai sauka a filin jirgin sama na Murtala Muhammed da ke Legas a yau.
A cewar sanarwar da mai ba shugaban shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai, Bayo Onanuga, ya fitar, Tinubu ya zaɓi komawa Nijeriya ta Legas ne domin girmama tunawa da marigayi MKO Abiola, wanda aka bayyana a matsayin gwarzon gwagwarmayar dimokuraɗiyya a Nijeriya.
Sanarwar ta ce a ranar ranar ’yancin Nijeriya, Shugaba Tinubu zai halarci bikin ƙaddamar da wani fim da aka shirya domin girmama Abiola, wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasa na Yunin 1993, a Wole Soyinka National Theatre da ke Iganmu, Legas.
Yayin da yake Legas, shugaban ƙasar zai kuma gudanar da wasu muhimman taruka da shugabannin siyasa da abokan hulɗarsa, yayin da ake ci gaba da shirye-shiryen babban zaɓen 2027.
Fadar shugaban kasa ta ce Tinubu ya bar Abuja a ranar 30 ga Agusta domin fara hutun aiki, inda ya fara kwashe mako guda a birnin London na Birtaniya kafin daga bisani ya wuce Paris.
A lokacin da yake Paris, shugaban ƙasar ya halarci wata liyafar cin abinci tare da Shugaban Faransa, Emmanuel Macron.
Haka kuma, Tinubu ya gana da wasu shugabannin ’yan kasuwa, ciki har da Vincent Bolloré, shugaban Bolloré Group, wanda harkokinsa na kafafen yaɗa labarai da fasahar zamani suka haɗa da Canal+, MultiChoice da Universal Music Group.
A ranar Litinin kuma, Shugaba Tinubu ya gana da Shugaban First Holdings, Femi Otedola, a wani ɓangare na tarurrukan da ya gudanar yayin zamansa a Faransa.
A makon da ya gabata, shugaban ƙasar ya halarci bikin sanya hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna tsakanin Gwamnatin jihar Ogun da kamfanin DP World domin gina tashar jiragen ruwa mai zurfi a yankin Ogun Waterside.
Yarjejeniyar ta kuma ƙunshi shirin samar da Blue Marine Economic Zone a yankin, domin bunƙasa harkokin tattalin arziki da suka shafi teku da tashoshin jiragen ruwa.
Fadar shugaban kasar ta ce kamfanin DP World, wanda ke cikin manyan kamfanonin da ke gudanar da tashoshin jiragen ruwa da harkokin sufuri a duniya, yana shirin zuba jarin dala biliyan bakwai ($7bn) wajen aikin tashar jiragen ruwa da yankin.
Bayan kammala tarurrukan siyasar da zai gudanar a Legas, Shugaba Tinubu zai koma Abuja, inda zai ci gaba da gudanar da ayyukan gwamnati.
