DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, September 15, 2026
HomeSiyasaSowore ya yi alƙawarin ba da wutar lantarki ta sa'o'i 24 idan...

Sowore ya yi alƙawarin ba da wutar lantarki ta sa’o’i 24 idan ya ci zaɓe

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar AAC, Omoyele Sowore, ya yi alƙawarin samar da mafi ƙarancin albashin ma’aikata na naira 500,000 a kowane wata ga ma’aikatan Nijeriya idan har aka zaɓe shi a matsayin shugaban ƙasa a babban zaɓen 2027.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa Sowore, wanda kuma fitaccen ɗan fafutuka ne kuma mawallafin kafar Sahara Reporters, ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da aka buga a ranar Lahadi yayin da yake fayyace manufofin jam’iyyar AAC na zaɓen 2027.

Ya ƙara da cewa gwamnatinsa za ta samar da wutar lantarki ta sa’o’i 24 a kowace rana, ta ba da ilimi kyauta a kowane mataki, ta gina gidajen al’umma miliyan ɗaya ga masu ƙaramin ƙarfi da matsakaita, tare da sauya dokokin haya domin kawo ƙarshen tilasta wa ma’aikata biyan kuɗin haya na shekara ɗaya ko biyu a gaba.

Sowore ya bayyana cewa, “Manufarmu ita ce tabbatar da adalci da daidaito. Nijeriya ƙasa ce mai arzikin gaske, amma an mayar da ‘yan Nijeriya matalauta da gangan ta hanyar cin hanci da rashawa, rashin ƙwarewa, da tsarin tattalin arzikin da aka kafa domin wadata tsirarun ‘yan siyasa da ‘yan kasuwa. Muna da niyyar sauya wannan lamari baki ɗaya.”

Ya jaddada cewa ma’aikatan Nijeriya ba za su ci gaba da karɓar albashin yunwa ba a yayin da sanatoci, gwamnoni, da masu muƙaman siyasa ke kwashe miliyoyin nairori a kowane wata. Ya kuma ce babu wani tattalin arziki na masana’antu da zai iya ci gaba ta hanyar dogaro da injin janareta, shi ya sa suka kuduri aniyar samar da hasken wutar lantarki na sa’o’i 24.

Ɗan fafutukar ya kuma yi alƙawarin bunƙasa aikin gona da sarrafa amfanin gona, ƙarfafa jami’an tsaro ta hanyar ƙara musu albashi, amfani da na’urori masu sarrafa kansu (drones), da kuma yaƙi da cin hanci da rashawa ba tare da sassauci ba domin ƙwato dukiyar al’umma da aka sace.

Sowore na ɗaya daga cikin ‘yan takarar shugaban ƙasa 18 da hukumar INEC ta sanar a hukumance a ranar Asabar, inda ya bayyana cewa jam’iyyar AAC za ta gudanar da kamfen ɗin da al’umma ne za su ɗauki nauyinsa maimakon dogaro da manyan ‘yan siyasa ko attajirai.

Ukashatu Wakili
Ukashatu Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili is a journalist and media professional serving as Deputy Managing Editor and Internship Coordinator at DCL Hausa. He has extensive experience in broadcast and digital journalism, with expertise in news reporting, editorial production, newsroom coordination and journalist training. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Usmanu Danfodiyo University, Sokoto.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata