Rundunar sojin saman Nijeriya (NAF) ta yi luguden wuta kan wasu ƴan bindiga da ake zargin suna ƙoƙarin wucewa daga jihar Zamfara zuwa Kebbi, yayin da jami’an tsaro ke ci gaba da fafatawa da ƙungiyoyin ƴan bindiga a yankin.
‘Yan bindigar da ake kiyasta yawansu da kusan 240, sun fito ne daga yankin Sangeko Gap da ke jihar Zamfara, kafin su nufi garin Makuku da ke Jihar Kebbi.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa ƴan bindigar na tafiya ne kan babura, inda suka raba kansu zuwa rukuni uku yayin da suke ƙoƙarin kutsawa cikin Kebbi.
Rahotanni sun ce sojojin Bataliyar COAS Intervention Battalion 3 ƙarƙashin tunduna ta 8 ta sojin ƙasa, tare da jami’an rundunar ’yan sandan sashin MOPOL, da kuma rundunar sama ta Operation FANSAN YAMMA, sun tunkari ƴan bindigar.
Hare-haren na sama na daga cikin matakan da rundunar ke amfani da su wajen dakile yunƙurin ƴan bindigar na kutsawa cikin al’ummomin da ke kusa da iyakar Zamfara da Kebbi.
Yawan ƴan bindigar da ake zargin sun kai mutum 240 ya haifar da fargaba a tsakanin mazauna yankunan da ke kusa da wurin da ake fafatawar.
Wasu mazauna yankunan sun fara barin gidajensu zuwa wuraren da suke ganin sun fi samun tsaro, yayin da jami’an tsaro ke ƙara ƙaimi wajen dakile ƴan bindigar.
Mukaddashin daraktan hulɗa da jama’a na rundunar sojin ƙasa, runduna ta 8, Operation FANSAN YAMMA, Laftanar Kanal Olaniyi Osoba, ya tabbatar wa Daily Trust faruwar lamarin.
Ya ce aikin sojojin na ci gaba da gudana, yana mai cewa za a fitar da ƙarin bayanai bayan kammala aikin.
A halin yanzu, jami’an tsaro na ci gaba da gudanar da hare-haren ƙasa da na sama domin hana ƴan bindigar samun damar shiga garuruwa da ƙauyukan da ke kan iyakar Zamfara da Kebbi.
Rundunar ta kuma shawarci mazauna yankunan da su kasance cikin taka-tsantsan tare da bin umarnin jami’an tsaro yayin da aikin ceto da dakile ƴan bindigar ke ci gaba.
