DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Monday, April 20, 2026
HomeLabaraiTinubu ya naɗa sabbin shugabannin makarantar horas da ‘ƴansanda da ke Wudil...

Tinubu ya naɗa sabbin shugabannin makarantar horas da ‘ƴansanda da ke Wudil a Kano

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya sake naɗa sabbin mambobi na kwamitin gudanarwa na makarantar horas da ‘yansanda wato ‘Nigeria Police Academy’ da ke Wudil a jihar Kano.

Wata sanarwa da fadar shugaban ta fitar, ta bayyana cewa a cikin sabbin naɗe-naɗen, shugaban ƙasar ya naɗa Ministan Harkokin ‘Yansanda, Ibrahim Gaidam, a matsayin shugaban kwamitin gudanarwar makarantar.

Sauran mambobin kwamitin sun haɗa da shugaban hukumar kula da ayyukan ‘yansanda, da Sufeto Janar, tare da wakilai daga ma’aikatun ilimi, kuɗi da shari’a na gwamnatin tarayya.

Haka kuma, shugaban ƙasar ya naɗa mutum shida daga yankuna shida na ƙasar domin wakiltar su a cikin kwamitin, wadanda suka haɗa da Babagana Zannah Adam daga Arewa maso Gabas, Emmanuel Torkuma Manger daga Arewa ta Tsakiya, da Maigari Abati Dikko daga Arewa maso Yamma.

Sauran su ne Dubem A. Obaze daga Kudu maso Gabas, Ajibogere Toyin daga Kudu maso Yamma, da kuma Udom Udo Ekpoudom daga Kudu maso Kudu, waɗanda za su kawo gudunmawarsu wajen tafiyar da harkokin makarantar.

Sanarwar ta ce wannan mataki na daga cikin ƙoƙarin gwamnati na ƙarfafa tsarin horo da inganta aikin rundunar ‘yansanda a Nijeriya.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata