Gwamnan jihar Kaduna Uba Sani, ya bayyana cewa ba za a iya kayar da shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu a zaɓen 2027 ba, sai dai idan za a jefa ƙuri’a a kafafen sada zumunta.
Gwamnan ya bayyana hakan ne cikin wani faifan bidiyo da gidan talabijin na Channels ya wallafa, inda ya ce idan aka bar zaɓe a hannun masu kada ƙuri’a a zahiri, Tinubu zai samu gagarumar nasara.
A cewarsa, “Idan za a yi zaɓe a Twitter, Facebook da Instagram, to zai sha kaye. Amma idan mutane ne za su kada ƙuri’a a zahiri, zai samu fiye da kashi 70 cikin 100 na ƙuri’u.”
Uba Sani ya kuma yi iƙirarin cewa jam’iyyar APC ba ta da wata hamayya mai ƙarfi a jihar Kaduna, yana mai cewa nasarorin da gwamnatinsa da ta Tinubu suka samu sun sa jihar ta zama kamar ta jam’iyya ɗaya, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
Gwamnan ya ƙara da cewa manufofin tattalin arziki da gyare-gyaren da gwamnatin tarayya ta aiwatar sun taimaka wajen ƙara kuɗaɗen da jihohi da ƙananan hukumomi ke samu, wanda hakan ya ba su damar gudanar da ayyukan ci gaba a matakin ƙasa.
Wannan na zuwa ne yayin da ake tunkarar babban zaɓen shekarar 2027, inda ake sa ran fafatawa mai zafi tsakanin jam’iyyun siyasa a ƙasar.
