DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Wednesday, May 13, 2026
HomeSiyasaJam'iyyar ADC ta sa N100m kudin fom din takarar shugaban kasa

Jam’iyyar ADC ta sa N100m kudin fom din takarar shugaban kasa

Jam’iyyar ADC ta sanar da fara sayar da fom ɗin takarar shugaban Nijeriya gabanin zaɓen 2027, inda ta kayyade farashinsa kan Naira miliyan 100.

Haka kuma ta fitar da jadawalin gudanar da zaɓukan fidda gwani, inda ta bayyana muhimman ranaku da suka shafi sayen fom, tantance ‘yan takara, sauraron ƙorafe-ƙorafe, da kuma gudanar da zaɓukan fidda gwani a matakai daban-daban na muƙamai.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labarai na ƙasa na jam’iyyar, Bolaji Abdullahi, ya fitar a ranar Lahadi, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Bisa ga jadawalin, za a fara sayar da fom ɗin takara daga ranar 5 ga watan Mayu zuwa 10 ga watan Mayu, 2026, yayin da za a karɓi fom ɗin da aka kammala cikewa daga ranar 11 zuwa 13 ga watan Mayun 2026.

Matakin kayyade irin wannan tsadar fom na shugaban ƙasa ya sake tayar da muhawara a tsakanin ‘yan Nijeriya, musamman dangane da yadda wasu ke ganin siyasa na ƙara zama ta masu hali kawai, wanda hakan na iya takaita damar matasa da masu ƙaramin ƙarfi shiga takara.

Sai dai a gefe guda, wasu na kare wannan mataki, suna masu cewa kuɗaɗen fom na taimakawa jam’iyyun siyasa wajen gudanar da harkokinsu, ciki har da shirya zaɓe da gudanar da ayyukan jam’iyya.

Ba wannan ne karo na farko da ake sanya irin wannan tsada ba, domin a zaɓukan da suka gabata ma wasu manyan jam’iyyu sun kayyade farashi mai nauyi ga fom ɗin shugaban ƙasa, lamarin da ya janyo cece-kuce a fadin ƙasar.

A yayin da lokaci ke kara matsowa, ana sa ran ƙarin jam’iyyu za su fito da tsare-tsarensu da kuma farashin fom ɗinsu, abin da zai kara fito da yanayin yadda siyasar 2027 za ta kasance.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata