Direbobi da masu ababen hawa a birnin Abuja sun roƙi gwamnatin Nijeriya da ta gaggauta daukar matakai domin rage radadin tashin farashin man fetur da ke ƙara jefa su cikin mawuyacin hali.
Rahotanni sun nuna cewa farashin man fetur ya tashi daga kusan Naira 900 a watan Fabrairu zuwa kimanin Naira 1,440 a kowace lita a halin yanzu, lamarin da ya haddasa karin kudin sufuri a fadin babban birnin.
Direbobi da fasinjoji sun bayyana cewa wannan karin farashi ya janyo matsin tattalin arziki, inda mutane da dama ke fuskantar wahala wajen biyan kudin zirga-zirga a kullum, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
Wasu direbobin sun ce sun dakatar da aiki gaba daya saboda rashin samun riba, yayin da wasu ke ci gaba da aiki cikin kunci, suna kokarin daidaita tsakanin kudin mai da kuma kudin da suke karba daga fasinjoji.
A bangaren fasinjoji kuwa, da dama sun bayyana cewa sun rage yawan zirga-zirgar da suke yi, yayin da wasu ke tilastawa kansu yin tafiya a kafa domin rage kashe kudi.
Masu ababen hawa sun jaddada cewa halin da ake ciki na iya kara jefa mutane cikin talauci idan ba a dauki matakin da ya dace ba.
