DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Wednesday, May 13, 2026
HomeSiyasa‘Yan majalisar wakilan Nijeriya 17 sun fice daga jam’iyyar ADC zuwa NDC

‘Yan majalisar wakilan Nijeriya 17 sun fice daga jam’iyyar ADC zuwa NDC

Akalla ‘yan majalisar wakilan Nijeriya 17 sun sauya sheka daga jam’iyyar ADC zuwa jam’iyyar NDC.

An sanar da sauya shekar tasu ne a zauren majalisar yayin zamanta a ranar Talata, inda a hannu guda aka sanar da sauya shekar Leke Abejide daga ADC zuwa jam’iyyar APC.

‘Yan majalisar da suka koma NDC sun hada da Yusuf Datti, Uchenna Okonkwo, Adamu Wakili, Thaddeus Attah, George Ozodinobi, Lilian Orogbu, Oluwaseyi Sowunmi, Peter Aniekwe, Mukhtar Zakari, George Oluwande da Munachim Umezuruike.

Sauran sun hada da Emeka Idu, Jesse Onuakalusi, Ifeanyi Uzokwe, Afam Ogene da Abdulhakeem Ado, kamar yadda gidan talabijin na Channels ya ruwaito.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata