Gwamnan Bauchi Bala Mohammed, ya ce jam’iyyun adawa da suka kaurace wa zaben kananan hukumomi a jihar sun ji tsoron faduwa ne.
Jaridar Punch ta ruwaito gwamnan ya bayyana hakan ne bayan ya kada kuri’a tare da matarsa Aisha a rumfar zabensa da ke Ɗan Kungibar, bakin dutse, a karamar hukumar Alkaleri.
Mohammed ya bayyana ‘yan adawar da suka kaurace wa zaben a matsayin masu tsoro, yana mai cewa da sun shiga zaben da sun samu damar gwada karfinsu da farin jininsu a tsakanin al’umma.
Ya ce zaben ya kasance wata dama ga jam’iyyun siyasa su auna karfinsu gabanin babban zaben 2027, yana mai jaddada cewa ba za a iya kafa gwamnati a tsarin dimokuradiyya ba tare da goyon bayan masu kada kuri’a ba.
Gwamnan ya kuma yaba da yanayin zaman lafiya da aka samu a lokacin kada kuri’ar, ya kuma nuna cewa an gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali.
Gwamna Bala Mohammed ya ce gwamnatin jihar na nan kan bakanta wajen tabbatar da dimokuradiyya da kuma bai wa jama’a damar amfani da ‘yancin da kundin tsarin mulki ya basu.
Gwamnan ya kuma jaddada muhimmancin kananan hukumomi wajen ci gaban jihar, saboda mafi yawan ayyukan da suka shafi rayuwar jama’a suna farawa ne a mataki na kasa-kasa, wato a kananan hukumomi.
Gwamnan ya ce jihar Bauchi ta ci gaba da gudanar da zabukan kananan hukumomi ba tare da tsallake wani zangon zabe ba, yana mai cewa sabon zaben zai kara karfafa dimokuradiyya a matakin kananan hukumomi.
Sai dai, wasu jam’iyyun adawa suna bayyana zaben a matsayin “zaben bogi” da ake zargin an shirya shi ne domin bai wa jam’iyyar da ke mulki dama.
Jam’iyyun da suka hada kai wajen kaurace wa zaben sun hada da ADC, AAC, SDP, da PRP.
A yayin wani taron manema labarai da suka gudanar a Bauchi, kakakin jam’iyyar ADC na kasa, Dakta Ladan Salihu, ya ce jam’iyyun sun dauki matakin ne tare saboda damuwar da suke da ita kan tsarin gudanar da zaben.
Jam’iyyun sun kuma nuna adawa da kudaden tantancewa da gudanar da harkokin takara da hukumar zaben kananan hukumomin jihar, BASIEC, ta gindaya, suna cewa kudaden sun yi wa jam’iyyun adawa nauyi.
Duk da kauracewar wasu daga cikin jam’iyyun, Gwamna Bala Mohammed ya ce kasancewar wasu jam’iyyun a zaben na nuna cewa dimokuradiyya na da karfi a jihar, tare da yaba wa masu kada kuri’a da suka fito domin amfani da damar da dimokuraɗiyya ta basu.
