DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Monday, September 14, 2026
HomeLabarai‘Yan daba sun sace abin bauta a wata cocin jihar Imo

‘Yan daba sun sace abin bauta a wata cocin jihar Imo

Wasu ‘yan daba sun kutsa cikin ɗakin ibada na Cocin St Mulumba da ke Owerri a Jihar Imo, inda suka sace abin ibada mai tsarki na Katolika.

Kamar yadda sanarwa daga Kansila na Cocin Katolika na Owerri, Rabaran Fada Patrick Mbarah ta bayyana, lamarin ya faru ne ranar Laraba 29 ga Afrilu, 2026, inda maharan suka kwashe abin bautar.

Jaridar the Sun ta ruwaito cewa maharan sun buɗe wani ɓangare na rufin ginin ne sannan suka shiga ta sama yayin da ake ruwan sama, kafin su aikata wannan aika-aika da cocin ta bayyana a matsayin tozarta wurin ibada.

Rabaran Fada Mbarah ya ce abin ya jawo baƙin ciki matuƙa, yana mai cewa wannan hari ya saba wa darajar wurin ibada da tsarkin abin da aka sace.

Bayan faruwar lamarin, Archbishop na Owerri, Most Rev. Lucius Iwejuru Ugorji, ya umarci mabiya cocin su gudanar da addu’o’in mako guda daga 1 zuwa 8 ga Mayu, domin neman gafara da tsarkake wurin.

Cocin ta kuma gargadi dukkan kiristoci da su bi ƙa’idojin da suka shafi adana da gabatar da wannan ibada, tare da jaddada cewa ba za a bar abin ibadar ba tare da kulawa ba.

Ukashatu Wakili
Ukashatu Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili is a journalist and media professional serving as Deputy Managing Editor and Internship Coordinator at DCL Hausa. He has extensive experience in broadcast and digital journalism, with expertise in news reporting, editorial production, newsroom coordination and journalist training. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Usmanu Danfodiyo University, Sokoto.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata