DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Wednesday, May 13, 2026
HomeSiyasaJam’iyyar ADC ta rasa Sanatoci biyu a majalisar Dattawan Nijeriya

Jam’iyyar ADC ta rasa Sanatoci biyu a majalisar Dattawan Nijeriya

Sanata Victor Umeh (Anambra) da Sanata Enyinnaya Abaribe (Abia) sun sanar da ficewarsu daga jam’iyyar ADC, suna danganta hakan da rikicin shugabanci da kuma sabanin cikin gida a jam’iyyar.

Umeh, wanda ke wakiltar mazabar Anambra ta Tsakiya, ya koma jam’iyyar NDC yayin da Abaribe, wanda ke wakiltar mazabar Abia ta Kudu, ya koma jam’iyyar Labour Party.

Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ne ya bayyana sauyin jam’iyyun a zaman majalisa ta hanyar karanta wasiƙu daban-daban, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

A cikin wasiƙarsa, Umeh ya ce ya yanke wannan hukunci ne bayan tattaunawa mai zurfi da masu ruwa da tsaki, ciki har da iyalansa, al’ummarsa, da kuma abokan siyasarsa.

Ya kuma jaddada aniyarsa ta ci gaba da ba da gudunmawa wajen bunƙasa ƙasa, yana mai cewa zai ci gaba da hidima ta hanyar sabuwar jam’iyyarsa.

A nasa ɓangaren, Abaribe ya ce ficewarsa daga ADC ta fara aiki nan take, tare da cewa ya ɗauki wannan mataki ne bisa abin da ya bayyana a matsayin rikicin shugabanci da ke ƙara tsananta a jam’iyyar.

Godswill Akpabio ya yi barkwanci kan yadda sauya sheƙar ‘yan majalisa ke ƙaruwa yayin da yake mayar da martani kan sabbin ficewar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata