Rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta musanta abinda ke yawo a shafukan sada zumunta cewa wani jami’in dan sanda yana daga wa ‘yan ta’adda hannu a cikin wani faifan bidiyo da aka dauka a jihar Katsina.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun ‘yan sandan Nijeriya, CSP Anietie Okokon Edem Iniedu, ya fitar, rundunar ta bayyana cewa mutanen da aka gani a cikin bidiyon ba ‘yan ta’adda ba ne, illa dai mambobin kungiyar masu sa-kai ta Vigilante Group da kuma mafarauta da aka yi wa rajista, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Sanarwar ta ce wadannan jami’an sa-kai suna aiki tare da hukumomin tsaro wajen gudanar da ayyukan yaki da miyagun laifuka a kananan hukumomin Musawa da Matazu na jihar Katsina.
Rundunar ta bayyana cewa bidiyon ya nuna yadda jami’in dan sanda ke tattaunawa da wadannan masu sa-kai yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa wani wurin aiki domin tallafawa ayyukan tsaro.
A cewar ‘yan sanda, duk wata magana da ke cewa mutanen da aka gani a bidiyon ‘yan ta’adda ne ko kuma jami’in dan sandan na magana da su da ɗaga musu hannu, karya ce kuma an kirkire ta ne domin yaudarar jama’a.
Sanarwar ta kara da cewa yada irin wadannan bayanan da ba su da tushe na iya haifar da fargaba a tsakanin al’umma, rage amincewar jama’a ga hukumomin tsaro tare da kawo cikas ga kokarin da ake yi na magance matsalolin tsaro.
Rundunar ta bukaci ‘yan Nijeriya da su yi watsi da bayanan da ake yadawa tare da dogaro da sahihan bayanai daga hukumomin gwamnati da tashoshin yada labarai sahihai.
Ta kuma yi gargadin cewa duk wanda aka samu yana kirkira ko yada bayanan karya da za su iya barazana ga zaman lafiya da tsaro, zai fuskanci hukuncin doka.
