Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya ce jam’iyyar APC a jihar za ta gudanar da sahihin zaben fidda gwani idan aka gaza cimma matsaya kan yunkurin fitar da ɗan takara ta hanyar sasanci da zai yi takara a zaben 2027.
Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin mayar da martani kan ce-ce-ku-cen da suka biyo bayan amincewa da tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar, Baba Mallam Wali, a matsayin dan takarar gwamna na sasanci a jam’iyyar.
Buni ya ce fitowar Baba Mallam Wali ta samo asali ne daga matsayar da aka cimma a taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar da aka gudanar ranar 23 ga Afrilu, 2026.
Ya ce idan ba a samu cikakkiyar fahimta tsakanin dukkan bangaroryi ba, APC za ta yi amfani da tsarin fidda ɗan takara ta hanyar zaɓe na kai tsaye domin bai wa kowa damar fafatawa a cikin adalci.
Gwamnan ya tuna cewa a shekarar 2019 shi ma an tsayar da shi a matsayin dan takara ta hanyar sasanci, amma bayan an kalubalanci matakin, sai aka gudanar da zabe inda ya samu nasara da gagarumin rinjaye.
Buni ya kara da cewa har yanzu shugabannin jam’iyyar na ci gaba da tattaunawa da masu neman takara da sauran masu ruwa da tsaki domin samar da maslaha cikin lumana kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Ya jaddada cewa hadin kai da zaman lafiya a APC su ne babban burinsa, yana mai cewa nasarar jam’iyyar a 2027 na bukatar cikakken hadin kai tsakanin mambobinta.
Sai dai wasu masu neman takarar gwamna guda shida a karkashin APC sun yi watsi da amincewa da Baba Mallam Wali a matsayin dan takarar da aka fitar ta hanyar sasanci, suna masu cewa zaben fidda gwani mai gaskiya da adalci kawai za su amince da shi.
Masu neman takarar da suka hada da Sanata Ibrahim Bomai, Bashir Machina, Kashim Tumsah, Mustapha Maihaja, Lawan Kolo Geidam da tsohon Sufeto Janar na ’Yan Sanda, Mohammed Alkali Baba, sun ce tsarin da aka bi ya saba wa dokar zabe da kundin tsarin APC.
Rahotanni sun ce bayan taron da suka yi a Abuja, masu neman takarar sun gana da Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, domin gabatar masa da korafinsu kan batun dan takarar da aka fitar.
