DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Wednesday, July 8, 2026
HomeLabaraiZulum ya jinjina wa sojojin Nijeriya bisa ceto mutane a Borno

Zulum ya jinjina wa sojojin Nijeriya bisa ceto mutane a Borno

Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum ya yaba wa sojojin Nijeriya musamman na Operation HADIN KAI bisa nasarar ceto mutane 360 da aka yi garkuwa da su a tsaunukan Mandara da ke kudancin Jihar Borno, inda ya ce aikin ya nuna jajircewa da kwarewar rundunar soji.

Gwamnan ya bayyana cewa aikin ya kara wa al’umma kwarin gwiwa tare da nuna ingancin hadin gwiwar hukumomin tsaro wajen yaki da ‘yan ta’adda, yana mai godiya ga Shugaba Bola Tinubu da shugabannin soji kan goyon bayan da suka bayar.

Ya kuma jaddada cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da tallafa wa rundunar soji da sauran hukumomin tsaro, tare da kira ga jama’a da su ci gaba da ba da hadin kai da sahihan bayanai domin kawo karshen ayyukan ta’addanci a jihar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata