Wasu da ake zargi ‘yan jagaliya ne sun far wa shugaban ƙaramar hukumar Owo a jihar Ondo, Mr. Tope Omolayo, inda suka lakada masa duka tare da tube masa kaya a bainar jama’a, lamarin da ya haifar da cece-kuce a yankin.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa ana zargin lamarin ya faru ne sakamakon wani rikici da ya ɓarke tsakanin ‘yan jam’iyyar APC a cikin jihar, inda aka ce sabanin ra’ayi tsakanin bangarori ya rikide zuwa tashin hankali.
Haka kuma rikicin na da nasaba da shirye-shiryen gudanar da tarukan jam’iyyar da kuma rabon mukamai a matakin ƙananan hukumomi, wanda a wasu lokuta ke haifar da sabani mai tsanani tsakanin magoya baya.
Majiyoyi sun bayyana cewa shugaban ƙaramar hukumar ya samu raunika sakamakon dukan da aka masa.
Hukumomin tsaro sun bayyana fara bincike kan lamarin domin gano waɗanda suka aikata harin da kuma tabbatar da an hukunta su bisa doka, duk da cewa ba a bayyana kama kowa ba zuwa lokacin hada wannan rahoto.
