Masarautar Zazzau ta dakatar da wani dagaci bisa zargin cuta da cin zarafin jama’a a wani lamari da ya shafi rabon gado a yankin Matarawa da ke ƙaramar hukumar Kudan a jihar Kaduna.
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa Sarkin Zazzau, Alhaji Ahmed Nuhu Bamalli ne ya bayar da umarnin dakatarwar bayan majalisar masarautar ta kammala bincike kan ƙorafin da aka shigar gabanta.
A wata sanarwa da jami’in yaɗa labarai na masarautar, Abdullahi Aliyu Kwarbai, ya fitar, an ce majalisar ta saurari ƙorafe-korafen da aka gabatar akansa kamar yadda aka saba sasanta rikice-rikice ba tare da zuwa kotu ba.
Sanarwar ta bayyana cewa an samu zargin cewa wasu daga cikin magadan wani mamaci an tauye musu haƙƙinsu, tare da hana wasu gadonsu.
Bayan cikakken nazari da bincike, majalisar masarautar ta bayar da umarnin dakatar da dagacin da ake zargi tare da kwato duk wasu kuɗaɗe da aka bai wa mutanen da ba su da hurumin karɓar wani kaso daga gadon.
Masarautar ta ce bayan an kammala kwato kuɗaɗen, Sarkin Zazzau ya miƙa su ga hakiman Kudan da Hunkuyi domin su koma yankin Matarawa su sa ido a sake rabon gadon cikin adalci.
Sarkin ya umarci hakiman da su tabbatar an gudanar da sabon rabon gadon bisa tsarin shari’ar Musulunci kamar yadda Alƙur’ani mai girma ya tanada.
Haka kuma, Sarkin ya gargadi dukkan hakimai da dagatai da su guji cutar da jama’a musamman a lamuran gado, yana mai jaddada cewa masarautar ba za ta lamunci zalunci ko son rai ba.
Ya kuma buƙaci hakimai su riƙa sanya ido sosai kan ayyukan da dagatai ke yi a yankunansu domin tabbatar da gaskiya da adalci wajen hulɗa da jama’a.
