DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, September 15, 2026
HomeSiyasa'Mun ba Aisha Yesufu tikitin Majalisar Wakilai amma ta ce ya yi...

‘Mun ba Aisha Yesufu tikitin Majalisar Wakilai amma ta ce ya yi mata ƙanƙanta’

Jagoran jam’iyyar NDC, Sanata Seriake Dickson, ya ce jam’iyyar ta bai wa fitacciyar mai fafutukar kare haƙƙin jama’a, Aisha Yesufu, damar tsayawa takarar kujerar Majalisar Wakilai, amma ta ƙi karɓa saboda tana ganin kujerar ta yi mata ƙanƙanta.

Dickson ya bayyana hakan ne yayin da rikicin cikin gida ke ci gaba da girma a jam’iyyar NDC, bayan Aisha Yesufu ta zargi shugabancin jam’iyyar da rashin adalci a tsarin fitar da ‘yan takara gabanin zaɓen 2027.

Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, Aisha Yesufu, wadda ta mara wa ɗan takarar shugaban ƙasa na NDC, Peter Obi, baya tun daga lokacin da yake jam’iyyar Labour Party har zuwa ADC da NDC, ta nuna sha’awar tsayawa takarar Sanata mai wakiltar Babban Birnin Tarayya (FCT). Sai dai daga bisani ta janye daga takarar tana mai zargin an samu kura-kurai a tsarin zaɓen fidda gwani.

Dickson ya ce zargin cewa jam’iyyar ta ware wasu mutane ba gaskiya ba ne. A cewarsa, shugabancin NDC ya yi ƙoƙarin ba fitattun ‘ya’yan jam’iyyar damar shiga takara, ciki har da Aisha Yesufu.

Ya ce, “Mun ba Aisha Yesufu tikitin Majalisar Wakilai amma ta ce kujerar ta yi mata ƙanƙanta.”

Sai dai Aisha Yesufu ta soki wasu kalaman Dickson a wata hira da ya yi a talabijin, tana mai cewa ya kamata shugabannin jam’iyyar su fi mayar da hankali wajen haɗa kan mambobi da ƙarfafa ‘yan takara maimakon jawo sabbin ce-ce-ku-ce.

A nasa ɓangaren, Dickson ya bukaci masu goyon bayan Peter Obi su taimaka wajen gina jam’iyyar maimakon kawo rikici, yana mai cewa duk wanda ke son Obi ya zama shugaban ƙasa bai kamata ya rika sukar NDC da shugabancinta ba.

Ukashatu Wakili
Ukashatu Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili is a journalist and media professional serving as Deputy Managing Editor and Internship Coordinator at DCL Hausa. He has extensive experience in broadcast and digital journalism, with expertise in news reporting, editorial production, newsroom coordination and journalist training. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Usmanu Danfodiyo University, Sokoto.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata