DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, July 7, 2026
HomeLabaraiFashola: Ban taɓa karɓar kuɗin tsaro ba a lokacin da nake gwamnan...

Fashola: Ban taɓa karɓar kuɗin tsaro ba a lokacin da nake gwamnan Legas

Tsohon Gwamnan Jihar Legas, Babatunde Fashola, ya bayyana cewa bai taɓa karɓar abin da ake kira kuɗaɗen tsaro ba a tsawon shekaru takwas da ya yi yana jagorantar jihar.

Fashola ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa kan shugabanci, dimokuraɗiyya da tsaro a taron The Platform, inda ya ce duk kuɗaɗen da aka kashe kan harkokin tsaro a Legas suna bi ne ta hanyar kasafin kuɗi da kuma gudummawar kamfanoni da mazauna jihar.

Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, Fashola ya ce ba ya fahimtar yadda ake maganar kuɗaɗen tsaro da ake bai wa gwamnoni kai tsaye, domin a cewarsa bai taɓa samun irin wannan kuɗi ba lokacin da yake gwamna. Ya ce duk kashe-kashen da suka shafi tsaro suna ƙarƙashin Ma’aikatar Kasafi da Tsare-tsare ta jihar.

Tsohon gwamnan ya bayyana cewa gwamnatin sa ta riƙa gudanar da tarurrukan tsaro kowane wata ba tare da yankewa ba tsawon shekaru takwas.

Ya ce ana amfani da Asusun Tallafa wa Tsaron Jihar Legas wajen tara kuɗaɗen tallafin jama’a da kamfanoni domin inganta ayyukan tsaro, kuma ana binciken asusun a kai a kai tare da sanar da jama’a yadda ake amfani da kuɗaɗen.

Fashola ya ƙara da cewa yaƙi da aikata laifuka ba ya taƙaitu ga amfani da makamai kawai, yana buƙatar manufofi masu kyau da sabbin dabaru.

Ya yi misali da yadda tsarin rage amfani da kuɗi a hannu da Babban Bankin Nijeriya ya ƙaddamar ya taimaka wajen rage wasu laifuka kamar fashi da makami da garkuwa da mutane a Legas.

Ukashatu Wakili
Ukashatu Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata