DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, July 7, 2026
HomeLabaraiBa zan taɓa sulhu da ‘yan ta’adda ba - Mutfwang

Ba zan taɓa sulhu da ‘yan ta’adda ba – Mutfwang

Gwamnan Jihar Filato, Caleb Mutfwang, ya bayyana cewa gwamnatinsa ba za ta taɓa shiga wata tattaunawa ko sulhu da ‘yan ta’adda da masu aikata laifuka ba, yana mai jaddada cewa za a ci gaba da matsa musu lamba har sai an dawo da zaman lafiya a jihar.

Mutfwang ya bayyana hakan ne ranar Juma’a a birnin Jos yayin wani taron tattaunawa na Ranar Dimokuraɗiyya, inda ya yi bayani kan ayyukan gwamnatinsa a fannoni da suka haɗa da tsaro, noma, samar da ruwa da kuma jin daɗin al’umma.

Gwamnan ya ce tattaunawa da masu laifi ba mafita ba ce, yana mai cewa jami’an tsaro za su ci gaba da korar su daga al’ummomin jihar.

Ya ƙara da cewa haɗin gwiwar da gwamnatin jihar ke yi da jami’an tsaro, sarakunan gargajiya da shugabannin al’umma ya fara haifar da sakamako mai kyau a yankunan da matsalar tsaro ta fi kamari.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Mutfwang ya ce an kama wasu da ake zargi da hannu a hare-haren da suka faru a jihar, kuma binciken da ake yi kan su na taimakawa wajen gano manyan hanyoyin sadarwa da ƙungiyoyin masu aikata laifuka ke amfani da su.

Ya kuma yabawa Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, bisa abin da ya kira goyon baya da umarnin da yake bai wa jami’an tsaro wajen yaƙi da matsalolin tsaro a faɗin ƙasar.

Gwamnan ya kuma bayyana cewa gwamnatinsa ta sayo manyan motocin taki kusan 5,000 domin tallafa wa manoma, tare da zuba sama da Naira biliyan 30 a ayyukan samar da ruwa a ƙananan hukumomin Langtang ta Kudu da Langtang ta Arewa.

Ya ce zaman lafiya da tsaro su ne ginshiƙan jawo masu zuba jari, yana mai bayyana cewa wasu masu zuba jari daga ciki da wajen ƙasa sun nuna sha’awar aiwatar da ayyuka kamar matatar mai da kuma katafaren wajen yanka dabbobi a jihar Filato.

Ukashatu Wakili
Ukashatu Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata