DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Wednesday, July 8, 2026
HomeLabaraiBabu dalilin ci gaba da tsare Nnamdi Kanu - Peter Obi

Babu dalilin ci gaba da tsare Nnamdi Kanu – Peter Obi

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, ya sake jaddada bukatarsa ta a saki shugaban kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu, yana mai cewa babu wani dalili da zai sa a ci gaba da tsare shi a gidan yari.

Peter Obi ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da ’yan Nijeriya da ke zaune a birnin Washington DC na kasar Amurka. Bidiyon tattaunawar ya bazu a kafafen sada zumunta, kamar yadda kungiyar Obidient Movement ta tabbatar.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa Obi ya ce tun da dadewa yake bayyana matsayinsa kan batun Kanu.

A cewarsa, ba daidai ba ne a tsare mutum saboda kalaman da ya yi a gidan rediyo ko kuma suka da yake yi wa wasu mutane. Ya ce a matsayinsa na dan siyasa, mutane na yawan kiransa da sunaye iri-iri amma bai dauki hakan a matsayin laifi ba.

Tsohon gwamnan Jihar Anambra ya kuma ce idan yana gwamnati zai fi amfani da tattaunawa wajen warware matsalolin masu tayar da ƙayar baya a sassan ƙasar. Ya ce ta hanyar sauraro da tattaunawa ne gwamnati za ta fahimci musabbabin korafe-korafen su tare da nemo mafita mai dorewa.

Sai dai a halin yanzu Nnamdi Kanu na zaman hukuncin daurin rai da rai bayan wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta same shi da laifukan da suka shafi ta’addanci da kuma kasancewa mamba a haramtacciyar kungiya a shekarar 2025.

Kanu ya daukaka kara kan hukuncin, yayin da lauyoyinsa ke neman a soke shari’ar da hukuncin da aka yanke masa.

Ukashatu Wakili
Ukashatu Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata