Gwamnatin Jihar Borno ta bayyana cewa sama da mutum 350,000 da ke da alaƙa da ƙungiyar Boko Haram sun fito daga dazuka sun miƙa wuya tun bayan ƙaddamar da shirin gyaran hali, da sake haɗa tubabbun mayaƙan ƙungiyar cikin al’umma.
Mai Bai Wa Gwamna Babagana Zulum Shawara kan Harkokin Tsaro, Birgediya Janar Ishaq Abdullahi mai ritaya, ne ya bayyana hakan a Maiduguri yayin bikin yaye tubabbun mayaƙa 720 da za a sake mayarwa cikin al’umma.
Kamar yadda Punch ta ruwaito, tsofaffin mayaƙan da aka sake haɗawa cikin al’umma sun kasance rukuni na tara na waɗanda aka tantance a matsayin masu ƙarancin haɗari. Dukkansu sun rantse da Alƙur’ani Mai Tsarki tare da bayyana shirinsu na komawa rayuwa ta lumana a yankunansu daban-daban na Jihar Borno.
Ishaq Abdullahi ya ce shirin da gwamnatin Borno ta fara a watan Yulin 2021 ya samu nasara sosai. A cewarsa, mutane 8,960 sun amfana da shirin a rukuni takwas da suka gabata, kuma da ƙarin mutum 720 da aka kammala musu shirin yanzu, adadin ya kai mutum 9,680 da aka sake haɗawa cikin al’umma.
Ya ƙara da cewa daga cikin waɗanda aka sake haɗawa akwai mata 992 da yara 2,050 da suka fito tare da mayaƙan.
Ya ce an ba su kayan fara rayuwa domin taimaka musu bayan sun bar sansanin, yayin da shugabannin al’umma da jami’an CJTF da mafarauta suka tantance su kafin amincewa da komawarsu cikin al’umma.
