Jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC) ta kafa kwamitin sulhu na ƙasa mai mambobi bakwai domin sasanta rikice-rikicen cikin gida da suka biyo bayan zaɓukan fidda gwani, a wani yunƙuri na ƙarfafa jam’iyyar gabanin babban zaɓen shekarar 2027.
Sanarwar na ƙunshe ne a cikin wata takardar haɗin gwiwa da shugaban jam’iyyar na ƙasa, Sanata Cleopas Moses, da sakataren jam’iyyar Ikenna Morgan Enekweizu, suka sanya wa hannu, kafin kakakin jam’iyyar na ƙasa, Osa Director, ya fitar da ita ga manema labarai.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa an ɗora wa kwamitin alhakin tattaunawa da ‘yan takarar jam’iyyar daga jihohi 36 na ƙasar domin warware korafe-korafe da suka taso bayan zaɓukan fidda gwani, tare da ƙarfafa haɗin kan jam’iyyar.
An naɗa fitaccen masanin tattalin arziki da siyasa, Farfesa Pat Utomi, a matsayin shugaban kwamitin, yayin da tsohon ɗan siyasa, Injiniya Buba Galadima, zai kasance mataimakin shugaba.
Sauran mambobin kwamitin sun haɗa da Mohammed Sanni Takori a matsayin mataimakin shugaba, Babatunde Alli a matsayin sakatare, sai Dudu Mamman Manuga, Salvador Adegoke Moshood da Alhaji Haruna Pai a matsayin mambobi.
Domin tabbatar da aikin sulhun ya kai ga dukkan yankunan da abin ya shafa, jam’iyyar ta kuma kafa ƙananan kwamitoci uku na shiyyoyi, waɗanda za su jagoranci sasanci a Arewa, Kudu maso Kudu da Kudu maso Gabas.
Rahotanni sun ce za a ƙaddamar da babban kwamitin ne da ƙarfe 12 na rana a ranar Alhamis a hedikwatar jam’iyyar ta NDC.
Shugabannin jam’iyyar sun bayyana kwarin gwiwar cewa aikin kwamitin zai taimaka wajen sasanta saɓanin da ke tsakanin mambobi, ƙarfafa haɗin kai da kuma gina tubali mai ƙarfi domin shirye-shiryen yakin neman zaɓen shekarar 2027.
