DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Monday, September 21, 2026
HomeLabaraiNAHCON ta musanta zargin karkatar da kujerun hajjin 2027

NAHCON ta musanta zargin karkatar da kujerun hajjin 2027

Hukumar aikin hajji ta ƙasa (NAHCON) ta karyata rahotannin da ke zargin an karkatar da kujeru 5,000 da aka ware domin aikin hajjin shekarar 2027, inda ta bayyana zarge-zargen a matsayin marasa tushe da ke da nasaba da son zuciyar ‘yan kasuwa.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa a cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar, ta bayyana cewa masu ruwa da tsaki na da haƙƙin neman ƙarin haske kan harkokin aikin hajji, amma ta buƙaci al’umma su bambance tsakanin sahihan bayanai da jita-jita.

NAHCON ta bayyana cewa zargin karkatar da kujerun an yi shi ne domin kawar da hankalin al’umma daga gazawar wasu kamfanoni wajen cika sharuɗɗan ƙa’idojin aiki, bin ƙayyadadden lokaci, da kuma loda bayanan maniyyata ta hanyar fasahar zamani kamar yadda ma’aikatar aikin hajji da umrah ta ƙasar Saudiyya ta gindaya.

Hukumar ta kuma nuna shakku kan sahihancin waɗanda suka fito da zargin, tana mai cewa rahoton ya dogara ne kan wasu mutane da ba a bayyana sunayensu ba da aka kira da “masu kula da harkokin kamfanonin sufuri masu zaman kansu.” Hukumar ta ƙara da cewa babu wata hujja ko ɗaya da aka gabatar da ke nuna cewa an saɓa wa dokokin aikin hajji na Saudiyya ko jagororin NAHCON wajen raba kujeru 5,000 da ake ce-ce-ku-ce a kansu.

Dangane da yadda aka raba kujeru 50,000 da Saudiyya ta amince wa Nijeriya a shekarar 2027, NAHCON ta bayyana cewa an ware kujeru 35,000 ga jihohi da babban birnin tarayya (FCT), yayin da aka bai wa kamfanoni masu lasisi kujeru 15,000. An raba waɗannan kujeru 15,000 ne ga kamfanoni masu zaman kansu da ke aiki a ƙarƙashin manyan kamfanoni bakwai da aka amince da su, daidai da ƙa’idojin Nijeriya da na Saudiyya.

NAHCON ta kuma ja hankali kan buƙatar yin rajistar maniyyata a shafin ‘Nusuk-Masar’ na Saudiyya, inda ta jaddada cewa hukumomin Saudiyya sun sanya ranar 26 ga watan Satumban 2026 a matsayin ranar ƙarshe ta loda bayanan maniyyata da na’urar ɗaukar hoton yatsu (biometrics). Hukumar ta ce ba ta da ikon tsawaita wannan wa’adi, don haka ta shawarci kamfanoni su mayar da hankali wajen loda bayanan abokan hulɗarsu kafin shafin ya rufe.

Hukumar ta gargaɗi cewa duk kamfanin da ya gaza cika waɗannan sharuɗɗa zai fuskanci hukunci mai tsauri da ya haɗa da dakatarwa, soke lasisi, ko hana shi shiga harkokin aikin hajji a gaba, tare da shawartar maniyyata da su gaggauta tabbatar da an loda bayanansu a shafin na Nusuk kafin cikar wa’adin.

Ukashatu Wakili
Ukashatu Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili is a journalist and media professional serving as Deputy Managing Editor and Internship Coordinator at DCL Hausa. He has extensive experience in broadcast and digital journalism, with expertise in news reporting, editorial production, newsroom coordination and journalist training. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Usmanu Danfodiyo University, Sokoto.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata