Ministan tsaro, Janar Christopher Musa mai ritaya, ya bayyana dabarun da jami’an tsaro ke amfani da su wajen ceto mutanen da aka yi garkuwa da su a wasu lokuta ba tare da an kama ko an kashe ‘yan ta’addar da suka sace su ba.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa ministan ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin da yake amsa tambayoyi a shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels, biyo bayan damuwar da al’umma ke nunawa kan yadda sojoji ke ceto mutane a jihar Kwara da wasu sassan arewacin Nijeriya ba tare da an kashe maharan ba.
Janar Musa ya bayyana cewa dabarar ta ta’allaka ne kan gano maɓoyar ‘yan ta’addar, toshe musu hanyoyin gudu, tare da yanke musu hanyoyin samun abinci, ruwa, man fetur, da sauran kayan masarufi da suke buƙata domin rayuwa, lamarin da ke tilasta musu tserewa su bar mutanen.
“Abin mamaki shi ne su ma ‘yan ta’addar ba sa son mutuwa. Ina fatan kun san da haka. Duk wannan ɗaukar makamai da suke yi, ba sa son mutuwa. Don haka da zarar an samu wani abu, ko da jirgi mara matuƙi (drone) ne ya zo, sai ka ga sun watse sun gudu. Abin da ke faruwa ke nan,” in ji Ministan tsaro.
Ministan ya kuma yi kira ga gwamnonin jihohi da su sake duba batun raba babura a matsayin tallafi, inda ya bayyana cewa galibi waɗannan babura na ƙarewa ne a hannun ‘yan ta’adda, lamarin da ke ba su damar kutsawa cikin daji tare da ɓacewa cikin sauƙi.
