DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Monday, September 14, 2026
HomeLabaraiFarashin man fetur na dab da rufewa 1,500 a Nijeriya

Farashin man fetur na dab da rufewa 1,500 a Nijeriya

Ana ci gaba da samun fargabar karin farashin man fetur, bayan matatar man fetur ta Dangote ta kara farashin sayar da man da naira 85 a kowace lita, sakamakon tashin farashin danyen mai a kasuwannin duniya.

Matatar ta kara farashin man fetur daga naira 1,265 zuwa naira 1,350 a kowace lita, wanda ke nuna karin kashi 6.7 cikin 100.

Hakan ya kara nuna farashin man na iya zuwa naira 1,500 a wasu sassan kasar.

Wannan karin farashi ya sa wasu manyan kamfanonin gidajen mai suka sake kara farashin da suke sayar da man fetur, inda yanzu masu ababen hawa a sassa daban-daban na Nijeriya ke sayen lita guda tsakanin naira 1,395 da naira 1,460.

Wannan lamari ya kara tayar da fargabar cewa farashin fetur zai iya ci gaba da karuwa idan farashin danyen mai a duniya da kuma kudin musaya suka ci gaba da tashi.

Masana harkar man fetur na fargabar cewa wannan karin farashi zai kara fadada tsananta wa ƴan ƙasa da kuma sayen kayayyakin.

Haka kuma, ana fargabar cewa Nijeriya da sauran kasashen duniya za su ci gaba da fuskantar tsadar man fetur na tsawon lokaci, ganin yadda yakin Amurka da Iran ke ci gaba da tsananta ba tare da alamun kawo karshen rikicin ba.

A makon da ya gabata, farashin danyen man Brent, wanda ake amfani da shi a matsayin ma’auni a kasuwannin duniya, ya kai dala 107 kan kowace ganga, abin da ya kasance mafi girma cikin makonni shida, Sai dai ya sauka zuwa dala 104, kamar yadda Jaridar Daily Trust ta ruwaito.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata