DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Monday, September 14, 2026
HomeLabaraiAn gano gawarwaki 9 bayan harin ’yan bindiga a Neja

An gano gawarwaki 9 bayan harin ’yan bindiga a Neja

Jami’an tsaro sun gano gawarwakin mutane tara a kan hanyar Wawa-Lumma da ke ƙaramar hukumar Borgu a Jihar Neja, bayan zargin cewa ’yan bindiga ne suka kashe su.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa kakakin rundunar ’yan sandan jihar Neja, SP Wasiu Abiodun, ya tabbatar da gano gawarwakin, yana mai cewa jami’an ’yan sanda da sojoji sun je wurin ne bayan an samu rahoton lamarin ranar Talata.

Gawarwakin mutanen an gano su ne a ranar Laraba, 12 ga Agusta, 2026, yayin da jami’an tsaro suka fara aikin kwashe su tare da kara tsaurara bincike da sintiri domin tabbatar da tsaron yankin.

SP Wasiu Abiodun ya ce tawagar ’yan sanda da sojoji ta musamman ce aka tura wurin, inda aka kwashe gawarwakin tare da fara aikin share fagen tsaro a yankin domin dakile duk wata barazanar ’yan bindiga.

Ya ce, “An tattara tawagogin ’yan sanda da sojoji na musamman zuwa wurin; an kwashe gawarwakin, sannan aka kara tsaurara aikin share fagen tsaro domin tabbatar da tsaron yankin.”

Lamarin ya faru ne kwanaki kadan bayan jami’an tsaro sun ceto mutane 308 da aka sace a hare-hare daban-daban a jihohin Kwara da Neja.

Daga cikin mutanen da aka ceto, 163 an sace su ne daga garin Woro da ke ƙaramar hukumar Kaiama ta Jihar Kwara, yayin da wasu 145 aka sace su a wani hari daban a Jihar Neja.

An ceto mutanen ne daga dajin Kainji Lake National Park da ke ƙaramar hukumar New Bussa ta Jihar Neja, a wani samame na hadin gwiwa da ya hada da rundunar soji, ’yan sanda, Hukumar DSS da National Counter-Terrorism Centre.

Ukashatu Wakili
Ukashatu Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili is a journalist and media professional serving as Deputy Managing Editor and Internship Coordinator at DCL Hausa. He has extensive experience in broadcast and digital journalism, with expertise in news reporting, editorial production, newsroom coordination and journalist training. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Usmanu Danfodiyo University, Sokoto.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata