DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, July 7, 2026
HomeLabaraiRundunar Sojin Nijeriya ta yi sauyin wurin aiki ga wasu manyan hafsoshi

Rundunar Sojin Nijeriya ta yi sauyin wurin aiki ga wasu manyan hafsoshi

Rundunar Sojin Nijeriya ta sanar da yin babban sauyi a muƙaman manyan hafsoshinta, inda aka sauya kwamandoji da jami’an horaswa da kuma wasu manyan jami’ai domin ƙarfafa ayyukan tsaro a faɗin ƙasar.

Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, mai magana da yawun rundunar sojin Nijeriya, Kanal Appolonia Anele, ta ce Shugaban Hafsoshin Soji, Laftanar Janar Waidi Shaibu, ne ya amince da sauyin domin inganta yadda rundunar ke fuskantar sabbin ƙalubalen tsaro.

Daga cikin sababbin naɗe-naɗen akwai Manjo Janar WM Dangana da aka naɗa a matsayin Babban Kwamandan Runduna ta 3 da kuma kwamandan Operation ENDURING PEACE, yayin da aka naɗa Manjo Janar EI Okoro a matsayin kwamandan Runduna ta 6 da Operation DELTA SAFE.

Rundunar ta kuma naɗa Manjo Janar SA Emmanuel a matsayin kwamandan Nigerian Army Space Command, matakin da rundunar ta ce zai ƙarfafa amfani da fasaha da sabbin dabarun yaƙi wajen tunkarar matsalolin tsaro.

Sauran naɗe-naɗen sun haɗa da Manjo Janar KE Chigbu a matsayin mataimakin kwamandan National Defence College, da Birgediya Janar U Ahmad a matsayin kwamandan Depot Nigerian Army da ke Zariya, yayin da rundunar ta ce sabbin jami’an za su nuna ƙwarewa da jajircewa wajen kare martaba da tsaron Nijeriya.

Ukashatu Wakili
Ukashatu Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata