Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya naɗa Abdulrazak Sa’ad Namdas a matsayin sabon Darakta Janar na Hukumar Raya Yankunan Kan Iyakokin Nijeriya (BCDA), tare da naɗa Patrick Obahiagbon da Chukwuma Umeoji a matsayin Daraktocin Kamfanin Niger Delta Power Holding Company (NDPHC).
Kamar yadda sanarwar mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ta bayyana, Namdas ya maye gurbin Dakorinama Alabo George wanda ya yi murabus domin neman muƙamin zaɓe a jiharsa.
Abdulrazak Namdas tsohon ɗan majalisar wakilai ne mai wakiltar mazaɓar Ganye/Jada/Mayo Belwa/Toungo a Jihar Adamawa, sannan ya taba zama mai magana da yawun majalisar wakilai ta 8. Haka kuma tsohon ɗan jarida ne kuma masani a harkar hulɗa da jama’a.
Sanarwar ta kuma ce shugaban ƙasar ya naɗa Patrick Obahiagbon a matsayin Daraktan tsare-tsare da harkokin kasuwanci na NDPHC, yayin da ya sake naɗa Chukwuma Umeoji a matsayin Daraktan kula da harkokin kamfanoni bayan ya taba yin murabus domin neman wata kujera ta siyasa a jiharsa.
Obahiagbon ya maye gurbin Injiniya Omoregie Ogbeide-Ihama wanda ya bar muƙaminsa domin neman wata kujerar siyasa a jiharsa, yayin da shugaban ƙasar ya buƙaci sababbin jami’an su yi aiki domin inganta ayyukan hukumomin da aka ba su jagoranci.
