DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Wednesday, September 23, 2026
HomeLabaraiAn kama masu damfarar mahajjata a Kebbi

An kama masu damfarar mahajjata a Kebbi

Rundunar ‘yan sandan Jihar Kebbi ta sanar da cafke wasu mutane huɗu bisa zarginsu da hannu a wata damfara da ta shafi sayar da kujerun aikin Hajjin bana tare da amfani da kayan bogi na aikin hajji.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar, CSP Bashir Usman, ne ya bayyana cewa jami’an tsaro sun kama babban wanda ake zargi mai suna Aminu Hassan Zauro tare da Tabiu Abubakar, Usman Attahiru da Mustapha Sani Zauro, yayin da ake ci gaba da neman wasu da suka haɗa da Bello Jos, Atiku Store, Umar Gimba da Usman Bunza.

Jaridar Punch ta ruwaito rundunar, ta ce bincike ya fara ne bayan Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kebbi ta kai ƙorafi cewa wasu maniyyata sun gano sunayensu ba su cikin jerin sunayen hukuma duk da sun biya kuɗaɗen kujera.

‘Yan sandan sun ce bincike ya nuna Aminu Hassan Zauro ya karɓi kuɗi har naira miliyan 8 da dubu 600 daga wani mutum da alƙawarin samar masa da kujeru biyu na aikin Hajjin 2026, alhali ba shi da wata huruma ko izinin gudanar da hakan.

Haka kuma, rundunar ta ce wanda ake zargin ya karɓi wani kaso na farko na naira dubu 690 daga wani mutum ta irin wannan hanya ta yaudara.

Sanarwar ta ƙara da cewa domin ɓoye laifin, waɗanda ake zargin sun samar da wasu kayan aikin hajji na bogi da suka haɗa da jakunkunan hajji, hijabai, zannuwa da katunan shaidar lafiya na jabu domin bai wa waɗanda suka damfara.

Kazalika ‘yan sandan sun ce sun ƙwato dukkan kayayyakin bogin tare da wata wayar salula kirar Tecno Android yayin gudanar da samamen.

Kwamishinan ‘yan sandan Jihar Kebbi, CP Umar M. Hadejia, ya yi gargaɗi ga maniyyata da su riƙa hulɗa kawai da Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta jihar ko jami’anta da aka tantance domin guje wa fadawa hannun masu damfara a nan.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata