DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, July 7, 2026
HomeLabarai'Janar Rabe Abubakar ya rasu a hannun ’yan bindiga'

‘Janar Rabe Abubakar ya rasu a hannun ’yan bindiga’

Gwamnatin jihar Katsina ta sanar da rasuwar tsohon babban jami’in soja mai ritaya, Manjo Janar Rabe Abubakar, wanda ya rasu yayin da yake tsare a hannun ’yan bindiga da suka sace shi.

A cikin wata sanarwa da Kwamishinan Harkokin Tsaro da Cikin Gida na jihar Katsina, Dakta Nasiru Mu’azu ya fitar, gwamnatin ta ce duk ƙoƙarin da jami’an tsaro da gwamnatin jihar suka yi na ceto shi cikin koshin lafiya, lamarin ya ƙare da rasuwarsa.

DCL Hausa ta ruwaito cewa gwamnatin jihar ta bayyana cewa marigayin ya rasu ne sakamakon matsalolin rashin lafiya da suka haɗa da ciwon sukari da hawan jini yayin da yake tsare a hannun masu garkuwa da mutane.

Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya jajanta wa iyalan marigayin da daukacin al’ummar Nijeriya, yana mai bayyana rasuwar a matsayin babban rashi ga jihar Katsina da ƙasa baki ɗaya.

Gwamnatin jihar ta kuma jaddada aniyarta ta ci gaba da haɗa hannu da gwamnatin tarayya da jami’an tsaro domin yaƙi da ’yan bindiga tare da tabbatar da an hukunta waɗanda ke da hannu a wannan lamari.

Ukashatu Wakili
Ukashatu Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata