DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, July 7, 2026
HomeLabaraiTinubu na da ƙudirin kawo ƙarshen rashin tsaro a Nijeriya – Oshiomhole

Tinubu na da ƙudirin kawo ƙarshen rashin tsaro a Nijeriya – Oshiomhole

Sanatan da ke wakiltar Edo ta Arewa, Adams Oshiomhole, ya bayyana cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu na da ƙudirin kawo ƙarshen matsalar rashin tsaro da ke addabar Nijeriya.

Oshiomhole ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a a Abuja yayin ƙaddamar da wani littafi da Kwamandan Hukumar NSCDC na Babban Birnin Tarayya Abuja, Olusola Odumosu, ya wallafa, inda ya yi martani kan masu zargin gwamnati da rashin nuna ƙwarin gwiwa wajen magance matsalar tsaro.

Ya ce Shugaba Tinubu na da ƙudiri sosai ta hanyar samar da ƙarin kuɗaɗe ga hukumomin tsaro, ciki har da amincewa da ƙarin kasafin kuɗi da majalisar dokoki ta ƙasa ta sahale domin ƙarfafa ayyukan tsaro a faɗin ƙasar.

A cewarsa, shugaban ƙasa ya kuma ɗauki wasu muhimman matakai kamar sauya shugabannin tsaro da kuma bai wa jami’an tsaro umurnin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma.

Sai dai ya bayyana cewa akwai buƙatar a tabbatar da cewa umurnin da ake bayarwa daga manyan hukumomi yana isa ga jami’an da ke bakin aiki.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata