DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, July 7, 2026
HomeLabaraiGwamnatin Gombe ta kori kamfanin sufuri bayan goyon bayan Pantami

Gwamnatin Gombe ta kori kamfanin sufuri bayan goyon bayan Pantami

Gwamnatin Jihar Gombe ta umarci kamfanin Gombawa Motors Nigeria Limited da ya fice daga babbar tashar Ibrahim Hassan Dankwambo Mega Park cikin sa’o’i 24, bayan zargin karya dokokin gudanar da tashar motar.

Kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito, sanarwar korar mai ɗauke da kwanan watan 25 ga Yuni 2026, wadda Manajan Daraktan tashar, Mayo Ani, ya sanya wa hannu, ta ce an ɗauki matakin ne bayan kwamitin kula da Mega Park ya zargi kamfanin da saba dokokin aiki sau da dama.

Matakin korar kamfanin ya zo ne kwanaki biyu kacal bayan kamfanin Gombawa Motors ya fito fili ya bayyana goyon bayansa ga ɗan takarar gwamnan PDP a Jihar Gombe, Farfesa Isa Ali Pantami, abin da ya haifar da zargin cewa matakin yana da alaƙa da siyasa.

Sakataren kamfanin, Muhammad Umar, ya bayyana korar a matsayin ramuwar gayya ta siyasa, yana mai cewa lokacin da aka ɗauki matakin ya ɗora ayar tambayoyi.

Ya ce, “Korarmu ta zo ne jim kaɗan bayan kamfanin ya fito ya bayyana goyon bayansa ga Farfesa Isa Ali Pantami. Wannan yana nuna yiwuwar sa hannun ƴan siyasa.”

Umar ya kuma ce sanarwar korar ba ta fayyace irin laifukan da ake zargin kamfanin da aikatawa ba.

A cewarsa, goyon bayan kowane ɗan siyasa hakki ne da kundin tsarin mulkin Nijeriya ya tanada, kuma bai kamata hakan ya zama dalilin hukunta kamfani ba.

Sai dai Babban Manajan Gombe Line, Dokta Sani Sabo, ya tabbatar da cewa an kori Gombawa Motors daga tashar, amma ya musanta cewa siyasa ce ta jawo matakin.

Ya ce kamfanin ba ya sama da doka, yana mai jaddada cewa an ɗauki matakin ne bisa ƙa’idojin gudanarwa na tashar.

Sanarwar korar ta kuma nuna cewa kamfanin ya kasa bin umarnin gudanarwa abin da ya jawo koke-koke daga sauran masu gudanar da harkokin sufuri a tashar.

Ukashatu Wakili
Ukashatu Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata