Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya gargadi masu son zuba jari a matatar man Dangote da kada su yi amfani da kuɗin makarantar ’ya’yansu ko kuma su sayar da gidajensu domin sayen hannun jarin.
Sarki Sanusi II ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis a Kano, yayin taron wayar da kan masu zuba jari kan shirin sayar da hannun jarin Dangote Refinery, inda ya shawarci jama’a da su zuba kuɗin da za su iya jurewa kin taba wa na wani lokaci.
Ya ce masu ƙaramin jari za su iya fara wa da kuɗaɗe kamar Naira 10,000, Naira 20,000 ko Naira 30,000, gwargwadon abin da za su iya warewa, maimakon ɗaukar kuɗin da suke buƙata domin muhimman bukatun su na rayuwa.
Sarkin ya kuma shawarci masu zuba jari da su kasance masu haƙuri, su riƙe hannun jarin na dogon lokaci maimakon saye da nufin samun riba cikin gaggawa.
Sanusi ya ce yana son al’ummar Kano su samu damar zama masu hannun jari a kamfanin da ɗan asalin Kano, Aliko Dangote, ya kafa, yana mai cewa bai kamata jihar ta kasance a baya wajen shiga kasuwannin jari da harkar hada-hadar kuɗi ba.
Ya kuma bayyana cewa wurin da matatar take ba shi ne abin da ke tabbatar da mallakarta ba, domin masu hannun jari ne ke mallakar kamfanin tare da cin moriyar ribar da yake samu. Ya bukaci wakilan ƙungiyoyi da kungiyoyin kwadago su wayar da kan mambobinsu game da damar zuba jari.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa Sanusi ya kuma bayyana ayyukan matatar Dangote, ciki har da samar da man fetur da taki, samar da ayyukan yi kai tsaye, tare da jaddada cewa masu zuba jari su yi la’akari da dogon lokaci wajen gudanar da jarinsu ta hanyar sha yanzu magani yanzu.
