Hukumar kula da albarkatun ruwa ta ƙasa (NIHSA) ta gargaɗi al’ummar jihohi 15 a faɗin Nijeriya kan yiwuwar fuskantar ambaliyar ruwa mai tsanani daga koguna tsakanin ranakun 19 zuwa 25 ga watan Satumban 2026, inda ta buƙaci mazauna yankunan da ke cikin haɗari da su gaggauta komawa wurare masu tudu da aminci.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa wannan gargaɗi na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa ta musamman kan ambaliyar ruwa da babban daraktan hukumar, Arch Umar Mohammed, ya fitar a ranar Asabar.
Umar Mohammed ya bayyana cewa hauhawar matakin ruwan koguna na iya haifar da ambaliya a ƙauyuka da garuruwa da dama, lamarin da zai jefa makarantu, cibiyoyin lafiya, kasuwanni, gonaki, da wuraren ibada cikin haɗari. Don haka ya buƙaci gwamnatocin jihohin da abin ya shafa da su gaggauta ƙaura da mazauna yankunan da ke gabar ruwa kafin ambaliyar ta auku.
Babban daraktan ya ce, “Ana hasashen samun ambaliyar ruwa mai ƙarfi a cikin kwanaki bakwai masu zuwa a jihohin Imo, Cross River da wasu jihohi 13. Ana sa ran ƙaruwar ruwan koguna zai haifar da ambaliya, don haka al’ummomin da ke kusa da magudanan ruwa su shirya ƙaura zuwa tudu.”
Hukumar ta lissafa jihohin da ke fuskantar wannan haɗari da suka haɗa da Imo, Cross River, Ebonyi, Benue, Anambra, Akwa Ibom, Edo, Bayelsa, Enugu, Kogi, Delta, Abia, Taraba, Rivers, da kuma Lagos. A cikin waɗannan jihohi, an gano dubban al’ummomi, daruruwan makarantu, asibitoci, da dubban kadada na gonaki da ke fuskantar barazanar ambaliyar.
A dalilin haka, NIHSA ta shawarci al’ummar da ke zaune a yankunan da ke kusa da koguna da magudanan ruwa da su ɗauki matakan kariya cikin gaggawa tare da matsawa zuwa yankuna masu tudu domin kare rayukansu da dukiyoyinsu.
