Tsohon Firaministan ƙasar Guinea kuma babban jigon ‘yan adawa a ƙasar, Sidya Toure, ya riga mu gidan gaskiya yana da shekaru 81 a duniya.
Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito daga majiyoyi na kusa da iyalansa cewa Toure ya rasu ne a ranar Juma’a a wani asibiti da ke birnin Paris na ƙasar Faransa, bayan ya shafe kusan makonni biyu yana jinya sakamakon rashin lafiya da ya yi fama da ita tun a birnin Abidjan na ƙasar Ivory Coast.
Marigayi Toure ya kasance shugaban babbar jam’iyyar adawa ta Union of Republican Forces (UFR), wadda yake jagoranta yana gudun hijira a Ivory Coast. Jam’iyyar ta UFR na cikin jam’iyyun siyasa 40 da gwamnatin mulkin soji ƙarƙashin Mamady Doumbouya ta rushe a watan Maris na wannan shekara.
Toure ya bar Guinea ne tun bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a watan Satumban 2021 wanda ya kawo Doumbouya kan karagar mulki. Daga bisani aka zaɓi Doumbouya a matsayin shugaban ƙasa a watan Disambar bara a wani zaɓe da bai haɗa da jam’iyyar UFR ko sauran manyan jam’iyyun adawa na ƙasar ba.
Tsohon Shugaban Ƙasar Guinea, Lansana Conte, ya naɗa Toure a matsayin firaminista a watan Yulin 1996, muƙamin da ya riƙe har zuwa watan Maris na 1999. A lokacin da yake kan mulki, ya mayar da hankali wajen aiwatar da sauye-sauyen fasalin gudanarwa da tattalin arziƙi tare da ƙarfafa alaƙar Guinea da hukumomin kuɗi na duniya.
Bayan saukarsa daga gwamnati, ya karɓi ragamar jam’iyyar UFR a shekarar 2000, inda ya zama babban ɗan adawa ga gwamnatin Conte da sauran gwamnatocin da suka biyo baya. Ya tsaya takarar shugaban ƙasa a shekarun 2010 da 2015 inda ya sha kaye a duka zaɓukan biyu.
Da yake nuna alhini a shafinsa na X, Firaministan Guinea mai ci, Amadou Oury Bah, ya bayyana Toure a matsayin mutum mai fice a tarihin siyasar ƙasar tsawon shekaru talatin, yana mai cewa ya kafa tarihi a matsayin jajirtaccen ɗan siyasa mai son kawo sauyi.
